A jiya Alhamis ne kafar CMG da ofishin MDD dake Geneva, da tawagar dindindin ta wakilan Sin dake Geneva, suka yi hadin gwiwar gabatar da bikin baje kolin al’adun Sin na musamman, a fadar kasashen duniya ta “palace of nations”.
Shugaban CMG Shen Haixiong, da shugaban kwamitin raya al’adu na ofishin MDD dake Geneva Francesco Pisano, da kuma zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Swizerland Chen Xu, sun halarci bikin tare da ba da jawabai.
- Jakadan Sin Mai Kula Da Shirin Kwance Damarar Makamai Ya Yi Kira Da A Tabbatar Da Ikon Kasashe Masu Tasowa Na Yin Amfani Da Kimiyya Da Fasaha Cikin Lumana
- Kamata Ya Yi Gwamnatin Amurka Ta Yi La’Akari Da Dalilan Karbuwar Gwamnan Jihar California A Kasar Sin
Wakiliyar musamman mai ba da shawara kan harkokin siyasa da huldar abokantaka, a ofishin babban jami’in MDD dake Geneva Lidiya Grigoreva, da dai sauran hukumomin kasa da kasa na MDD dake Geneva, da zaunannun wakilan kasashe fiye da 30 sun halarci bikin.
Cikin jawabin da ya gabatar, Shen Haixiong ya ce, al’adun Sin na bayyana mutuncin Sinawa, da kuma bayyana abubuwa mafi kyau a cikin al’adun bil Adama. Kaza lika kasar Sin na dukufa kan farfado da al’adun ta a sabon zamani. A matsayin kafa mafi girma dake watsa labarai a dukkanin fannoni na dandalolin daban-daban, Shen ya ce CMG na sauke nauyin dake wuyansa na shaida ci gaban al’adu, da ingiza mu’amalar al’adu, ban da wannan kuma, tana kokarin hada tunani da kimiyya da fasaha tare, ta yadda al’umommin kasa da kasa za su sada zumanta, da tutunbar juna, don zamanintar da al’ummar duniya cikin hadin kai.
Yayin bikin na musamman na wannan karo, mai taken “Mafarin al’adun Sin da ci gabansa”, an yi amfani da kimiyya da fasahar zamani, don jagorantar masu kallo, ta yadda za su fahimci al’adun Sin masu tsawon tarihin fiye da shekaru 5000, da ma yadda ake samun ci gaba bisa wannan tushe.
Sannan a jiya Alhamis 26 ga wata ne, kafar CMG ta kuma gudanar da wani biki don kaddamar da nune-nunen “Journey Through Civilizations” wato hanyar fahimtar wayewar kai a cibiyar al’adun kasar Sin dake Alkahira, babban birnin kasar Masar. Mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong ya yi jawabi ta kafar bidiyo.
A yayin jawabinsa, Shen Haixiong ya bayyana cewa, a cikin dogon tarihi, kyawawan wayewar kan kasar Sin da na tsohuwar kasar Masar sun ba da gudummawa sosai ga ci gaban wayewar kan dan Adam. Bisa ga kyakkyawan tsarin shawarar wayewar kai ta duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, jama’ar kasar Sin suna aiki tukuru don gina al’ummar kasar mai wayewar kai ta zamani, da sa kaimi ga neman sabon ci gaban wayewar kan dan Adam. Shen Haixiong ya kara da cewa, CMG zai tabbatar da aikin watsa labaru, da yin kirkire-kirkire, da yada wayewar kan kasar Sin, da karfafa mu’amalar al’adu tsakanin Sin da kasashen Larabawa, da sa kaimi ga yin shawarwari tsakanin al’ummomin Sin da kasashen Larabawa, da ba da hikimomi da karfi wajen bunkasa fahimtar juna da dankon zumunci tsakanin jama’ar Sin da kasashen Larabawa, da inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da kasashen Larabawa. (Masu Fassarawa: Amina Xu, Bilkisu Xin)