Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da wasu shirye-shiryen talabijin mafi kyau da ya shirya a birnin Lima, hedkwatar kasar Peru a ran 30 ga wata.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya nuna cewa, a watan Yunin bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana yayin da ya yi shawarwari da takwararsa ta kasar Peru madam Dina Boluarte a nan birnin Beijing cewa, za a ci gaba da yayata dadadden dankon zumunci tsakanin al’ummun kasashen biyu da zurfafa hadin gwiwarsu, da ma gaggauta huldarsu ta abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni zuwa sabon mataki. Wannan bikin da CMG ya gabatar tare da hadin gwiwar kafofin yada labarai na Peru, na nufin tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wanda zai zurfafa cudanyar al’ummun biyu da kara dankon zumuncinsu, da ma bude wani sabon babi na nagartacciyar huldarsu nan gaba. (Amina Xu)