A jiya Laraba 18 ga watan nan ne aka fitar da jerin sunayen takardun hadin gwiwa da aka daddale, yayin taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na uku, wadanda suka kunshi takardu goma da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya daddale, tare da hukumomin gwamnatoci, da wasu kafofin watsa labarai na kasashe 9.
Yayin taron kolin da aka gudanar, shugaban CMG Shen Haixiong, ya daddale takardun hadin gwiwa da jami’an kasashen Habasha, da Pakistan, da Thailand, da Myamar, da Indonesiya, da Masar, da Hungary, da Serbia da kuma Chile. (Mai fassara: Jamila)