A yau ne, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya gudanar da rahaza karo na 2 na shagalin murnar sabuwar shekarar 2025 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. Bayan da aka yi rahaza karo na 1, an kara inganta shirye-shiryen wake-wake da raye-raye da na masu amfani da sabbin fasahohin zamani, ta yadda aka iya gabatar da shirye-shiryen shagalin yadda ya kamata. Siffar dandalin shagalin ta yi kama da abin nuna fatan alheri na al’adun gargajiya na Sin wato Ruyi, wanda ya hada dandalin shagalin da bangaren masu kallon shagalin, ta hakan za a sa kaimi ga tabbatar da masu kallon a wurin sun kara jin dadin yanayin shagalin.
Haka zalika kuma, an tanadi salon gabatar da shagalin murnar sabuwar shekarar 2025 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ga masu lallurar gani da ji a karo na farko don saukaka musu jin dadin shagalin. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp