CMG Ya Kaddamar Da Ginin Babbar Cibiyar Ayyukan Yada Shirye-shirye Mai Fasahar UHD

Babban rukunin gidan radiyo da talabijin na kasar Sin (CMG), a ranar Juma’a ya kaddamar da gina wata babbar cibiyar tantance ayyukan shirye shiryen yada labarai ta kasar Sin, inda za’a dinga samarwa da kuma gabatar da ingantattun bidiyo da murya mai fasahar (UHD) a birnin Shanghai dake gabashin kasar ta Sin.

Cibiyar, ita ce irinta ta farko a kasar Sin baki daya. CMG, tare da hadin gwiwar jami’ar Shanghai Jiao Tong, da kwalejin nazarin watsa labarai, da kula da gudanarwar gidan radiyo da talabijin ta kasa za su gudanar da aikin.

Aikin zai mayar da hankali ne wajen samar da ingantattun fasahohin zamani na bidiyo da murya wadanda ake iya samarwa karkashin sabon tsarin fasahar zamani ta intanet, musamman fasahohin bidiyo da murya na UHD, da ingantattun fasahohi na VR, da fasahar kwaikwayon tunanin dan adam ta AI.

Kaddamar da gina cibiyar wani muhimmin aiki ne na tabbatar da cigaban muhimman fasahohin zamani na ‘5G+4K/8K+AI,’ da kuma gina sabon tsarin shirye shiryen yada labarai mafi inganci a duniya, don watsa shirye shirye da kuma samun babban tasiri, Shen Haixiong, shugaban CMG kana mataimakin shugaban sashen yada labarai na kwamitin tsakiyar jamiyyar Kwaminis ta kasar Sin, shi ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da bikin ginin cibiyar. (Daga CRI Hausa, mai fassarawa: Ahmad Fagam)

Exit mobile version