• English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

CMG Ya Shirya Taron Yada Ruhin Taron Wakilan JKS Karo Na 20 A Zanzibar

byCMG Hausa
3 years ago
CMG

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

Cibiyar dake tsara shirye-shirye da harsunan nahiyoyin Asiya da Afirka ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake yankin Zanzibar da hukumar watsa labarai na yankin, sun shirya taron yada ruhin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 mai taken “Sabon tafarki da makoma ta bai daya” a yankin Zanzibar na kasar Tanzaniya a ranar 26 ga wannan wata, agogon kasar, taron da ya samu halartar babban karamin jakadan kasar Sin dake yankin Zhang Zhisheng, da babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai da matasa da al’adu da wasannin motsa jiki ta gwamnatin juyin juya hali ta Zanzibar Fatima Hamad Rajab, da shugaban hukumar watsa labarai ta yankin Hassan, da shugabanni da manema labarai na manyan kafofin watsa labarai sama da 20 dake yankin.

Yayin taron, wakilan kasar Sin sun yi bayani kan babban sakamako da babbar ma’anar babban taron wakilan JKS karo na 20, da fasahohin da JKS ta samu wajen gudanar da harkokin kasa, duk wadannan sun samu yabo da amincewa daga mahalartan taron.

Babban karamin jakadan kasar Sin dake yankin Zanzibar Zhang Zhisheng shi ma ya gabatar da jawabi yayin taron, inda ya bayyana cewa, kasar Sin wadda ta shiga sabon tafarki na zamanintar da kasa mai bin salon tsarin gurguzu tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Tanzaniya, domin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka ta bai daya.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai da matasa da al’adu da wasannin motsa jiki ta gwamnatin juyin juya hali ta Zanzibar Fatima Hamad Rajab ita ma ta yaba wa babban sakamakon da al’ummun Sinawa suka samu karkashin jagorancin JKS, inda ta bayyana cewa, taron da aka shirya zai taimaka wa kafofin watsa labarai na yankin Zanzibar wajen kara fahimtar manufofin tafiyar da harkokin kasa na JKS, haka kuma zai taimakawa kafofin watsa labarai na Zanzibar yayin da suke gabatar da labaran dake shafar kasar Sin, da ingiza hadin gwiwa da cudanya a fannoni daban daban tsakanin sassan biyu wato kasar Sin da Zanzibar. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

October 7, 2025
Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   
Daga Birnin Sin

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

October 6, 2025
Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka
Daga Birnin Sin

Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka

October 6, 2025
Next Post
NDLEA Ta Cafke Wani Basaraken Kauye Da Wasu Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Cafke Wani Basaraken Kauye Da Wasu Kan Safarar Miyagun Kwayoyi

LABARAI MASU NASABA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa

October 7, 2025
Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

October 7, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

October 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version