Cristian Pulisic: Chelsea Ta Sayi Babban Dan Wasa, In Ji Mourinho

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa kungiyar Chelsea tayi nasara data doke kungiyoyin Arsenal da Liberpool wajen siyan dan wasa Cristian Pulisic.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dauki dan wasan Borussia Dortmund, Christian Pulisic kan fam kudi miliyan 58, amma zai ci gaba da wasa a matsayin aro a kungiyar zuwa karshen kakar wasa ta bana.
Dan wasan mai shekara 20, dan asalin kasar Amurka wanda aka danganta shi zai koma kungiyoyin Liberpool da Arsenal a baya can, ya je Dortmund a shekarar 2015 a matashin dan kwallo.
Pulisic ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Amurka kwallo tara a wasa 23 da ya buga mata tun bayan daya fara kasar ta Amurka wasa kuma kawo yanzu yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da ake ji dasu a kasar Jamus.
“Pulisic dan wasa ne mai kyau kuma matashin dan wasa wanda zai dade yana buga wasa a kungiya kuma ya cancanta da kudin da aka siyeshi duba da yadda yakje buga wasa tun yana matashi” in ji Mourinho
Sai a watan Yunin shekara ta 2020 ne ya kamata yarjejeniyar Pulisic ta kare a kungiyar Borrusia Dortmund, amma yanzu ya zama mallakin Chelsea zai kuma ci gaba da buga wasa aro a Dortmund din.

Exit mobile version