Cristiano Ronaldo ya zura kwallo a raga inda ya taimakawa Al Nassr ta doke Al-Ahli da ci 4-3 a gasar cin kofin Saudi Pro ranar Juma’a.
Dan wasan mai shekaru 38 a yanzu ya zura kwallaye 15 a wasanni 14 da ya buga wa Al Nassr a kakar wasa ta bana.
- Babu Adawa Tsakanina Da Messi – Cewar Ronaldo
- Ronaldo, Neymar Da Benzema Na Fatan Lashe Gasar Zakarun Asia
Kwallon farko da Ronaldo ya zura a wasan na ranar Juma’a ta kasance mai ban mamaki.
Nasarar ta ranar Juma’a ita ce nasarar da Al Nassr ta samu ta biyar a jere a gasar, kuma Al Nassr sun koma matsayi na biyar, inda suke gaban Al-Ahli da ke da bambancin kwallaye.
Yanzu haka dai kungiyoyin biyu sun koma tazarar maki uku tsakaninta da kungiyar Al-Ittihad wadda ke da maki 18 a wasanni bakwai. Al-Hilal ce ta biyu da maki 17.