Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace ta samu babbar nasara a tarihinta bayan ta doke Manchester City da ci 1-0 a wasan ƙarshe na FA Cup da aka buga a filin Wembley da ke birnin Landan.
Wannan shi ne kofin farko da Crystal Palace ta taɓa lashe kofin tun bayan kafuwarta.
- Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta
- Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina
Eberechi Eze ne, ya zura ƙwallon da ta bai wa Palace nasara a minti na 16 da fara wasa.
Sabon ɗan wasan City, Omar Marmoush, ya samu dama mai kyau amma ya ɓarar da bugun fenariti a minti na 36.
Wannan kuma shi ne kofin ƙarshe da Manchester City ke fatan lashewa a wannan kakar.
Yanzu haka, ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta za ta kammala kakar ba tare da lashe kofi ba.
A wannan kakar kuwa, Liverpool ce ta lashe gasar Firimiya, yayin da Real Madrid ta fitar da Manchester City daga gasar Zakarun Turai.














