Hussaini Yero" />

Cutar Korona: DFID Ta Gudanar Da Bita Ga “Yan Jarida A Zamfara

Hukumar DFID a shirinta na bangaren lafiya,ta gudanar da taron bita ga ” yan jarida na kwana biyu a Gusau , akan yaki da annobar cutar Korona.
Jami’n shirin Lafiya na jihar Zamfara, Dakta Mannir Bature Tsafe, ya bayyana cewa, “Sun shirya wannan taron bitar ne dan wayar da kan ‘yan jarida wajan dauko labarin annobar Korona da ta addabi duniya.
“A jawabinsa Dakta Mannir ya tabbatar da cewa, duk wani shiri ko aikin yana samun nasara ne ta kafafen yada labarai, kuma a wannan lokacin duk wani shirin da ba zai tafi kafada da kafada da “yan jarida ba lallai ba zayi nasara ba inji Dakta Mannir .
“Dan haka mu kaga ya dace karkashin hukumar DFID shirinta mai taken Lafiya, muka shirya maku bita akan yadda zaku dauko rahotanin ga mai dauke da annobar Korona a nan jihar Zamfara.
“Dakta Mannir ya kuma kara da cewa, ” Hukumar DFID ,a jihohi takwas ta ke gabatar da shirinta mai taken Lafiya, don yaki da annobar cututuka .wadannan jahohin sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Barno, Yobe, Lagos da Zamfara. kuma wannan shirin ya bada gudunmuwa wajen yakar annobar Korona na tsawoñ wata shida a jihohin, Zamfara, Katsina , da Legas.
Masana akan kiwon Lafiya ne suka kabara da kasidu akan cutar da kuma yadda ‘Yan jarida ya kamata su dauko labarai a inda annobar Korona ta ke.
Mataimakin Edita na Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya watau ( NAN ) da ke Gusau, Abubakar Ahmda da Shugaban Kamfanin Sadarwa na Tanda ,Dakta Anas Anka suna da cikin wadanda suka gabatar da kasidu a wajan taron .
Shugabar yaki da annobar cututuka ta jihar Zamfara , Darka Rabi Usman ta bayyana cewa , ” ya kamata “Yan jaridu su taikama masu wajan wayar da akan al’umma a lokacin da annoba ta barke dan dakile ya dowar ta .
“Dakta Rabi Usman ta kuma tabbatar da cewa , gwamnati na iyaka kokarin ta wajan dakile annobar Korona a wannan jiha tamu .
Jami’in hukumar NCDC , na jihar Zamfara ,Tajudini Ismail ya bayyana cewa , ” Abunda ke bashi mamaki shine haryanzu wasu na ganin cewa babu cutur Korona ,kuma wannan wautane dan abu bai samaika ba kace babu shi .dan haka mu ke kira ga ku ‘Yan jaridu da Ku cigaba da wayar da kan al’umma illar wannan annobar Korona da kuma bin shawarwarin likitoci dan dakile samuwar ta .
Kwamishina Lafiya ,Yahaya Muhammad Kanoma ya jinjina ma wannan hukumar DFID da shirinta na Lafiya da ta shirya wannan bita ga “Yan jaridu kuma lallai duk abunda babu ‘Yan jaridu ba zai kai gaciba .dan haka ma’aikatar lafiya zata tafi da ku kafada da kafada dan samun nasara ayyukan ma’aikatar .

Exit mobile version