Jihar Lagos ta samu rahoton kamuwar matasa 10 da cutar Mashaƙo tsakanin ranar 1 ga Janairu zuwa 27 ga Maris 2025, yayin da hukumomin lafiya ke ƙara ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.
Kwamishinan lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa ana iya samun rahoton cutar har sama da 15 a rana. Daga cikin samfurorin da aka yi wa gwaji guda 76 an samu 10 da aka tabbatar da sun kamu, yayin da sauran samfurorin 63 sakamakonsu ya ke lafiya. Kwamishinan ya ƙara da cewa cutar ta afkawa ƙananan hukumomi da dama, inda Eti-Osa ta fi yawan wanda abin ya shafa.
- Kisan Mummuken Cutar Mashako A Nijeriya Da Sassan Duniya
- Fasaha Da Balagar Harshen Manzon Allah (SAW) II
Abayomi ya bayyana cewa hukumomin lafiya suna gudanar da aikin tantancewa da bayar da magani cikin gaggawa, Gwamnatin jihar ta ci gaba da samar da tallafi, tare da samar da magani kyauta a asibitoci na gwamnati, inda aka tabbatar da samar da kayan da ake buƙata wajen tattara bayanai da haɗin kai tare da hukumar kiwon lafiya ta ƙasa da ta duniya.
Matakan da aka ɗauka suna tasiri wajen daƙile yaɗuwar ƙwayar cutar a cikin makon nan na baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp