Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, sama da yara 520 ne suka rasu a sanadiyyar barkewar cutar mashako da ta bulla a fadin jihar a kwanakin baya.
Daraktan hukumar kiwon lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Muhammed Nasir Mahmoud, ya tabbatar da wannan adadin a jihar a wani taron kwana daya kan wayar da kai da aka shirya wa kafafen yada labarai a jihar kan bullar cutar.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Jigilar Dalibai 158 Zuwa Jihohi 5 A Karkashin Shirin Musayar Dalibai
- Majalisar Kano Za Ta Karrama Dan Adaidaitan Da Ya Maida Wa Dan Chadi Miliyan 15 Da Ya Tsinta
Nasir wanda ya sanar da hakan a ranar Talata ya ce, tun bayan barkewar ta a watan Disambar 2022, jihar ta samu adadin bullar cutar da ta kai 8700 da kuma wata 6300.
Cutar ta yadu a kananan hukumomi 39 cikin kananan hukumomin 44 da ke fadin.
Ya kara da cewa, yara kashi 27 cikin dari ne kacal aka yi wa rigakafin cutar, wanda adadin su, ya kai kashi 7.5 da kuma wasu kashi 59.9 a cikin dari da ba a yi masu allurar rigakafin ba.