Cutarwa Ce Iyaye Mata Da Suka Yi Akan Kin Shayar Da Jariransu

Wani kwararre  a babban asibitin tarayya na Owerri babban birnin jihar Imo Dokta Emeka Nwaolisah, ya bayyana cewar mata wadanda suka ki shayar da jariransu, ba wai kawai sun cutar da su jariran bane, har ma da al’umma.

Nwaolisah ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Abuja cewar “Shi al’amarin shayar da Jarirai Nonon Iyayensu, wata hanya ce ta samar da yara masu hazaka nan gaba”.

Ya bayyana cewar wasu mata wadanda suke kin shayar da Jariran su, ba domin komai ba sai saboda kawai suna tsoron kada Nonon su ya fadi.

Amma duk da hakan ya kara da cewar “kodai  sun shayar da Jarieran nasu Nono, ko kuma basu shayar ba, dole ne watarana shi Nonon ya fadi, saboda dai akwai shekaru da kuma irin hali ko yanayin da za a iya shiga.

Ya cigaba da bayanin cewar “Yana da kyau mata wadanda suka haihu su shayar da ‘ya’yansu Nono kamar dai yadda ya kamata, saboda dai daga karshe shi Nonon yana iya fadi ko an sha ko kuma ba a sha ba, saboda ai komai na lokaci ne.

“Ya kamata mata su gane cewar mata yakamata su gane ita ko kuma shi al’amari shayar da Nono kamar yadda ya dace, yana samar da hazikan yara zuwa gaba, wadanda al’umma za su yi alfahari dasu a gaba. Wannan kuwa ya kasance hakan ne saboda shi Nonon Uwa ya kunshi wasu sinadarai wadanda Allah ya yarda su kasance a cikin shi ruwan Nonon.

“Saboda shi Nonon Uwa kamar yadda ya kara jaddadawa, ya kunshi dukkan abubuwan da shi Jariri ke bukata saboda ingantattar rayuwa,wdda ba zata kasance da matsala ba, don haka ita mata ko kuma su Matan da sukka ki shayar da Jariran su basu ma kyautta ma al’umma ba”.

Don haka ne ma shi kwararre ko kuma masani akan al’amuran lafiya da suka shafi mata da kananan yara, ya yi kira da mata su tabbatar da ko kuma abin ya kasance masu kamar dole ne, saboda wannan wata hanya ce ta samar da al’umma masu ingancin lafiya.

Kamar dai yadda ya kara yin bayani shi al’amarin shayarwa yana da muhimmanci, saboda shi Nonon Uwa ya kunshi madara wadda ita ma tana tattare da sinadari wanda ake kira Docosahedanoic Acid (DHA) da kuma wasu saura wadanda suma suna taimakawa wajen al’amarin daya shafi koyon abubuwa na shi jaririn, wato yadda zai iya kasancewa zuwa gaba.

“Daga karshe dai kamar yadda abin ya kan kasance shi Nonon ko wacce mata yana iya kasancewa cikin wani yanayi sannu a hankali, wannan kuma babu yadda za a iya kauce ma shi al’amarin Allah, wannan bai kamata ya zama dalillin da su za su hana su abubuwan da sukje da damar a basu kamar dai yadda ya bayyana.’’

Shi dai makon shayarwa ko kuma abinda aka fi sani da ranar shayarwa ta duniya, ana yin  bikin ranar daga 1  zuwa 7 ga watan Agusta, a kasashe kusan 120 na duniya, na duniya an kuma fara yin hakan ne tun shekarar 1992. An kuma yi hakan ne saboda a bayar da kwarin gwiwa saboda inganta lafiyar Jarirai a kasashen duniya.

Taskan bikin na wannan shekarar shine “ Taimaka ma Iyayae mata saboda su rungumi shi al’amarin shayarwa gadan- gadan” an kuma zabi shi taken su ma kan su Iyaye mata su gane muhimmancin yin hakan ne wato shi al’amarin na shayarwar.

 

 

 

Exit mobile version