Da ɗimi-ɗiminsa: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Gobe Talata 1 Ga Watan Jimada Akhir

Daga Idris Umar, Zariya

Majalisar Sarkin Musulmi da ke Sokoto, ta ayyana ranar Talata 4/1/2022 a matsayin 1 ga watan Jimada Akhir 1443 AH.
Sarkin Malaman Sokoto kuma Sakataren Majalisar,  Yahaya Muhammad Boyi ne ya sanar da hakan wakilin LEADERSHIP Hausa cikin daren nan.

Dama dai Sarkin Musulmi ya umarci al’ummar Musulmi su duba tsayuwar sabon watan daga yau Litinin da ta kasance 29 ga Jimada Ula.

Exit mobile version