A wani gagarumin ci gaba na yaki da ‘yan ta’adda, an kashe ‘yan bindiga 80 a wani samame da jami’an tsaron hadin gwiwa suka kai a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
An kai hare-haren ne a ranar Asabar 4 ga watan Junairu, 2025, a wasu fitattun sansanoni a yankunan Kadoji, Matso-Matso, Bagga, Dogon Marke, da Takatsaba.
- Harin ‘Yan Bindiga: ‘Yansanda Sun Ceto Matafiya 18 Da Dabbobi Da Dama A Katsina
- Shekaru 62 Na Gwamnan Kano Sun Yi Albarka – Auwal Lawal
Rundunar Sojojin Sama na ‘Operation FANSAN YAMMA’ ne suka aiwatar da wannan samamen, tare da sojoji na Birged 17 na Sojojin Nijeriya, ‘yansanda, DSS, da kuma ‘yan banga na yankin.
Bisa ga sahihan bayanan sirri, dakarun hadin gwiwa sun kai farmaki a sansanonin da suka kasance matattarar ta’addanci a kananan hukumomin Jibia, Batsari, da Batagarawa na jihar.
Baya ga ‘yan bindiga 80 da aka kashe, an kuma jikkata wasu da dama, tare da lalata abubuwan hawan su da kayayyaki da suke amfani da su wurin kaddamar da ta’addancinsu, lamarin da zai rage musu karfi matuka wajen kai hare-hare kan ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Dr. Nasir Muazu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya yaba da kokarin jami’an tsaro, inda ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na maido da zaman lafiya a jihar da ma fadin Arewa baki daya.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar na yin aiki kafada da kafada da jami’an tsaro da al’ummomin yankin domin tabbatar da zaman lafiya.