Wata babbar kotun jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja, babban birnin jihar, ta dakatar da Ohinoyi na masarautar Ebira, Alhaji Ahmed Muhammed Tijani Anaje daga kujerar sarauta.
In ba a manta ba dai, tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ne ya nada Anaje a matsayin Ohinoyi na masarautar Ebira a watan Janairu, 2024.
- NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano
- Kano Pillars Ta Dakatar Da Kocinta Na Tsawon Makonni Uku
Sai dai, Mai shari’a Salisu Umar, alkalin babbar kotun tarayya ta 6 da ke Lokoja, a hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, ya bayar da umarni ga wanda ake kara (Anaje) da ya daina bayyana kansa a matsayin sarki na Masarautar Ebira.
Ko da yake har yanzu kotun ba ta bayar da cikakken bayani kan hukuncin ba, amma an gano cewa, shari’ar mai lamba HCO/05C/2024, Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutane biyu ne suka shigar da ita, inda suke kalubalentar hukuncin tsohon gwamnan jihar na Kogi.
Sai dai, jin ta bakin Ohinoyi, Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje, ya ci tura yayin da wayoyin sa duk suke kashe a lokacin rubuta wannan rahoto.