Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, a ranar Alhamis, ta tabbatar da nasarar da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar Gombe.
Kotun ta ce, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ta tabbatar da sahihanci da ingancin zaɓen gwamnan Inuwa ta yi daidai domin shi ne halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
- Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukaci Lauyoyin Su Mayar Da Kwafin Takardun Shari’ar
- NNPP Ta Bukaci Majalisar Shari’a Ta Kasa Ta Binciki Hukuncin Da Aka Yanke Wa Gwamna Yusuf
Kan hakan kotun ɗaukaka ƙarar ta kori ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta Jibrin Barde suka shigar da ke ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen na tabbatar da gwamna Inuwa na jam’iyyar APC.
Idan za a tuna dai hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta shelanta cewa Gwamna Muhammad Yahaya shi ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da ƙuri’u 342,821.
Yayin da ta ce Muhammad Jibrin Barde na PDP ya samu ƙuri’u 233,131 a zaɓen da aka fafata a jihar.
Amma Barde ya garza kotu domin ƙalubalantar nasarar Inuwa da iƙirarin cewa ba a bi dokar zabe ta 2022 ba wajen gudanar da zaɓen.
Sai dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar mai Alkalai uku a ƙarƙashin Justice S.B. Belgore, ta kori ƙarar da cewa bata da inganci.
Hakan ya sa ɗan takarar PDP ya sake garzayawa kotun ɗaukaka ƙara.
Kazalika, a ranar Alhamis ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar bisa cewa, korafin PDP bai da makama.