Jarumin Kannywood Abubakar Waziri ko kuma Baba Rabe kamar yadda wasu ke kiranshi ya bayyana batutuwa da dama da su ka shafi jaruman fim, yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum da kuma yadda mutane ke kallonsu, Baba Rabe a wata hira da ya yi da DW ya ce akwai bukatar malamai su shigo cikin harkar Kannywood ka’in da na’in domin yanzu wani lokaci ne da mutane sunfi mayar da hankalinsu wajen kallon fina-finai fiye da wa’azozin malaman musulunci.
Abubakar Waziri wanda ya ce shi haifaffen birnin Zaria ne a Jihar Kaduna, ya yi karatu a makarantu da dama har ma da Jami’ar Ahmadu Bello inda ya samu shaidar kammala karatun Diploma a bangaren Al’adun gargajiya, bayan harkar fim ni ma’aikacin gwamnati ne inda nike aiki da ‘Abuja Council For Art And Culture’, amma tunda farko na fara aiki a Jami’ar Ahmadu Bello a matsayin dan wasan kwaikwayo a sashen Al’adun Gargajiya na makarantar inji shi.
- Nijeriya Za Ta Nuna Gyare-gyaren Tattalin Arzikin Gwamnatin Tinubu A Taron Kasuwanci A Faransa
- Taro Na Uku Na Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ya Yi Zama Na Biyu
Ya kara da cewar kafin shiga masana’antar Kannywood na yi tafiye tafiye da dama wajen wakiltar Nijeriya a kasashe daban-daban da su ka hada da Amurka, China, Afrika Ta Kudu, Korea Ta Arewa, Korea Ta Kudu da sauran kasashen waje duk dai a fannin raye raye da wasan kwaikwayo, kuma cikin ikon Allah yanzu kuma gani a masana’antar Kannywood a matsayin jarumi.
Da yake amsa tambaya a kan yadda wasu ke daukar jaruman masana’antar Kannywood a matsayin wasu mutane masu girman kai, Abubakar Waziri ya ce ko kusa wannan magana ba gaskiya bace, misali mu jaruman fim da muka kasance abinda bature ke kira ‘public figure’, muma muna da abubuwan da muke son aiwatarwa a rayuwar yau da kullum, idan na fito daga gida idan ba na yi fuska na yi tafiya ta ba, mutane da dama kan zo wajena domin daukar hotuna ko kuma yi mani tambayoyi a kan wasu fina-finai da na yi.
Idan hakan ta faru wani lokacin mutum ba zai samu damar da zai aiwatar da abin da ya fito gida domin ya aiwatar ba, don haka kamata yayi mutane su fahimce mu a maimakon su koma gefe su na kiranmu da masu ji da kai, Waziri ya ci gaba da cewar wannan dalili ne ya sa mutane ke yi masu kudin goro a duk lokacin da wani daga cikinsu ya aikata abinda ba daidai ba a maimakon a dora ma wanda ya yi laifin shi kadai sai ace ai duka yan fim haka suke.
Daga karshe Abubakar Waziri Bado ya yi kira da a maimakon malamai su koma gefe su na zagi yan fim kamata ya yi ace su shigo cikin harkar a dama dasu, domin kuwa yanzu wani lokaci ne da ake ciki inda da dama mutane sun fi kallon fina-finai fiye da yadda su ke kallon karatuttukan malaman addini, saboda haka su shigo a hada karfi da karfe wajen kara tsaftace wannan masana’antar don kuwa ni ma kaina da ace ba jarumin fim bane ni , to da tabbas zan zama malamin addinin musulunci saboda ina matukar sha’awar ganin al’umma ta gyaru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp