Rundunar sojojin saman Nijeriya ta kashe ‘yan bindiga da dama tare da lalata maboyarsu da sansanoninsu a jihar Katsina.
Duk da cewa, harin ya gamu da tangarda biyo bayan rahotonnin da ke cewa, an samu asarar rayukan fararen hula, amma babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan zargin.
- Hukumar Kula Da Ayyukan Duba-gari Ta Kasa Za Ta Karrama Shugaba Tinubu
- Fina-finai Masu Dogon Zango A Masana’antar Kannywood: Ci Gaba Ko Akasin Haka?
Kakakin NAF, AVM Olusola Akinboyewa a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce rundunar sojin saman ‘Operation FANSAN YANMA’ (AC OFY), a ranar 15 ga watan Fabrairun 2025, ta kai wani samame cikin nasara a tsaunin Yauni, Unguwar Zakka a karamar hukumar Safana, jihar Katsina.
Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina.
AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuna cewa, an kai harin ta’addanci a wani sansanin PMF da ke cikin al’umma, inda aka ce, ‘yan bindigar sun kashe jami’an PMF biyu da CEC hudu.