Da Dimi-diminsa: Gwamnatin Bauchi Ta Sa Dokar Hana Zirga-zirga A Fadin Jihar

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da sanya dokar hana Zirga-zirga a fadin jihar, a cewar takardar da kwamishinan yada labarai na jihar ya saki, dokar za ta fara aiki ne daga jibi Alhamis, sannan gwamnatin ta roki al’ummar da su kiyaye dokar; dakile yaduwar annobar Coronavirus ta take cin duniya kamar wutar daji.

In ba a manta ba, gwamnan jihar Bauchi din yana daga cikin gwamnonin da suka kamu da cutar Coronavirus, shi da wani amininshi, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa mutum 2 a fadin jihar.

Exit mobile version