Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a ranar Alhamis ya gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Taron wanda aka dade ana tsammani tun bayan da jiga-jigan suka fafata a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya samu halartar wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar PDP.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Ahmed Umaru Fintiri na jihar Adamawa da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia.
Duk da cewa har yanzu ba’a bayyana makasudin taron ba, LEADERSHIP ta ruwaito cewa an shirya taron ne domin neman goyon bayan Wike ga Atiku a zaben 2023 mai zuwa.
Ganawar na zuwa ne jim kadan bayan da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gana da gwamna Wike da abokansa tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da kuma tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke a birnin Landan a ranar Alhamis.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp