Sabuwar Firaministan Birtaniya, Liz Truss ta yi murabus.
Truss gaba daya watanni biyu ta shafe a kan mukaminta.
- Wata Kungiya Ta Yi Barazanar Maka Kungiyar Kwadago A Kotu A Jihar Kebbi
- Gwamnatin Kogi Ta Maka Dangote A Kotu Kan Takaddamar Kamfanin Simintin Obajana
Ta doke Rishi Sunak da kuri’u 81,326 zuwa 60,399 a zaben cikin gida bayan Boris Johnson ya yi murabus a watan Yuli.
‘Yar majalisar ta kasance shugaba ta hudu na jam’iyyar Conservative a gwamnatin Birtaniyya tun daga shekarar 2015, inda ta yi alkawarin fitar da damar Birtaniya ta hanyar samar da ci gaba da kuma kawar da cikas da ke kawo wa kasar baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp