ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Cafke Ma’aikatan NIMC Na Bogi Da Ke Yi Wa Wadanda Ba ‘Yan Nijeriya Katin Dan Kasa

by Sadiq
4 years ago
Bogi

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa dakarunta tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya NIS da rundunar ‘yansandan Nijeriya sun cafke wasu jami’an bogi biyu na hukumar ba da shaida katin dan kasa a Jamhuriyar Nijar. 

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a taron mako biyu kan ayyukan sojojin Nijeriya tsakanin 6 zuwa 20 ga Oktoba, 2022 a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis.

  • Da Dumi-Dumi: Firaministan Birtaniya, Liz Truss Ta Yi Murabus 
  • Wata Kungiya Ta Yi Barazanar Maka Kungiyar Kwadago A Kotu A Jihar Kebbi

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gagamari a Jamhuriyar Nijar a lokacin da suke yi wa wadanda ba ‘yan Nijeriya rijista ba tare da sanya su cikin ma’adanar bayanai ta Nijeriya ba.

ADVERTISEMENT

Danmadami ya zayyana kayayyakin da jami’an tsaro suka kwato daga hannun wadanda ake zargin da suka hada da: Na’urar rajista ta kasa (NIN), na’urar buga kati, na’urar bin diddigin kwamfuta da injin janareta da dai sauransu.

“A ranar 13 ga Oktoba, 2022, sojoji tare da rundunar ‘yansandan Nijeriya da jami’an NIS sun kama wasu jami’an hukumar kula da bayanan sirri na kasa (NIMC) guda 2 da ake zargin na bogi ne.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

“An bayyana cewa wadanda ake zargin sun ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Gagamari da ke Jamhuriyar Nijar ne domin yin rijistar wadanda ba ‘yan Nijeriya ba a sansanin ‘yan gudun hijirar.

“Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da na’urar rijista ta kasa (NIN), na’urar buga kati, na’urar bin diddigin kwamfuta da injin janareta da dai sauransu.”

Da yake tsokaci game da ci gaban yayin gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida, tsohon Daraktan DMO, Manjo-Janar Benard Onyeuko, ya ce za a bankado aniyar jami’an bogi idan an kammala bincike.

Ya ce wannan wani sabon abu ne da sojoji suka samu don haka ya kamata a yaba wa rundunar soji.

“Rundunar sojin ta cancanci a yaba mata bisa nasarar da ta samu wajen kame wadannan masu laifi a kasar waje.”

Onyeuko, wanda yanzu shi ne Daraktan sayan kayayyaki a hedikwatar tsaro ya kara da cewa, “A cikin wannan yanayi, yanzu an kama su, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike, wanda ya hada da duk wanda ke da alaka da wannan badakala.

Ya kara da cewa, “Za a bayyana sakamako idan aka kammala bincike, amma a lura cewa wannan wani sabon abu ne, kuma ina ganin ya kamata a yabawa sojojin kasar kan hakan.”

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Tsarin Zamanintar Da Aikin Noma Na Sin Ya Gaggauta Bunkasuwarta Da Ma Duniya Baiki Daya

Tsarin Zamanintar Da Aikin Noma Na Sin Ya Gaggauta Bunkasuwarta Da Ma Duniya Baiki Daya

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.