Akalla gidajen burodi 40 ne suka rufe tare da shiga yajin aiki a babban birnin tarayya kan tsadar farashin kayayyakin aiki da kuma karin haraji da kudin wutar lantarki da aka musu.
Wasu gidajen burodi da aka ziyarta ba a bude su ba saboda tsadar kayan aiki da haraji da wasu hukumomin gwamnati suka musu.
- An Kaddamar Da Alkur’ani Da Aka Fassara Zuwa Harshen Igbo A Abuja
- Sama Da Mutum 150 Ke Hannun ‘Yan Bindiga A Jibiya – Shugaban Karamar Hukumar
Wasu daga cikin gidajen burodin da suka rufe sun hada da Abumme bakery Ltd. da ke Lugbe, Hamdala Bakery a Kuje, Harmony Bite Bakery a Karu da Doweey Delight Bakery Ltd a Kubwa.
Sauran sun hada da Merit Baker da me Mpape, Funez Baker a Orozo, Slyz Bakery a Wuse Zone 2, da sauransu.
Ishaq Abdulraheem, Shugaban Kamfanin burodi na Abuja Master Bakers, ya bayyana cewa abin damuwa ne ganin cewa gidajen burodin da ke Abuja ba za su iya jurewa tsadar kayan aiki ba.
Ya ce akasarin ‘yan kungiyar sun rasa abin yi, yayin da ma’aikata ma sun rasa aikin yi saboda rufe gidajen burodin da aka yi.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta shiga tsakani, ta kuma duba hukumomin gwamnati da ke kawo cikas ga harkokin kasuwancin burodin.
Mutane da dama sun koa kan yadda ake ci gaba da samun karin tashin farashin burodi a ko da yaushe.
Sai dai gidajen burodi da dama sun alakanta hakan, da tsadar da fulawa da sukari suka yi, wadanda sune kashin bayan abubuwan da ake amfani da su wajen samar da burodin.