Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewar ta janye dokar da ta kafa na hana baburan Adaidaita Sahu bin wasu manyan titunan jihar.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba DanAgundi, ya fitar a yau Laraba.
- Kwarto Ya Harbe Mijin Matar Da Yake Lalata Da Ita
- Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima
Tun da fari, gwamnatin Kano, ta ce ta sanya dokar ne don kawo gyara a harkar sufuri a jihar.
Wasu daga cikin titunan da aka hana baburan Adaidaita Sahu sun hadar da titin Tal’udu zuwa Gwarzo, titin Hadeja zuwa Gezawa, titin Ahmadu Bello, titin gidan gwamnatin jihar da sauransu.
Wannan lamari ya janyo rudani da maganganu na bacin rai a tsakanin mutane musamman masu amfani da ababen hawa na Adaidaita Sahu.
Sai dai gwamnatin ta yi nazari kam janye dokar har zuwa nan da wani lokaci biyo bayan kiranye-kiranyen jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp