Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka

by
4 years ago
in Uncategorized
4 min read
Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Har Yanzu Messi Ya Fi Kowa Daukar Albashi A Tamaula

Dakarun MNJTF Sun Yi Barin Wuta Kan ‘Yan Boko Haram Sun Kashe 300 A Tafkin Chadi

Hakika wannan magana haka ne take ga duk wanda yake asalin an haife shi a Karkara ne, ya kuma tashi a cikinta, tun yana karami har shekarun hankali suka fara shigarsa. Ko shakka babu zai san abinda ake nufi da Jinka, tun farkon yadda ake fara yinta, har akai ga sa mata abinda wasu ke kiran danboto, wanda sai bayan an yi yantar shi yayin ko kuma cuci, to bayan an kammala rufe ita jinkar wadda ginin kara ne aka yi cikin fasaha, aka kuma yabe shi da kasa , daganan kuma aka sa ma ta suna Tafarfara. Idan kuma za asa ta lokacin rufe Tafarfarar sai an gaiyato mutane sun zo sun taimaka wajen dora ita Jinkar bisa Tafarfarar, wadda a lokacin kuma ta zama daki ke nan. Haka ne aka samo ita wannan Karin magana ko kuma salon dake nuna hannu daya baya daukar Jinka, kamar dai yadda aka fara bayanin.
Hakkokin gwamnati wadanda suka kamata tayi wa al’ummarta, saboda dama ai alhakin yin hakan ke nan wanda ya rataya kan ta, kamar samar da ruwan sha, gina makarantu, hanyoyi, asibitoci magudanun ruwa, wuraren zuba shara, da dai sauransu. Duk da yake ita gwamnati walau kodai ta tarayya, ko kuma ta Jihohi da kuma Kananan Hukumomi suna kokarinsu wajen samarwa al’ummarsu abubuwan more rayuwa, wadanda zasu sa rayuwarsu ta kasance abar sha’awa ga kowa. Sai dai kuma duk da yake gwamnatoci suna iyakar kokarinsu wajen taimakawa wajen samar da kyakkyawar rayuwar al’umma amma akwai wasu mutane da suke ganin wannan kokarin da gwamnatocin suke yi, su duk abin kamar bai burge su ba , saboda basu kulawa da ayyukan da ake yi masu, wadanda zasu kawo masu ci gaban su. Maimakon hakan ma su kan wulakanrar da abubuwan kamar yadda dai wasu daga cikin ku masu karatu, kuka taba gani a wasu wuraren da Allh ya baku damar zuwa.
An dai tashi an san da cewar a Alkaryu da Kauyuka ana da kungiyoyin kulob kulob wadanda sune ke taimakawa gwamnatoci wajen kokarin da suke yi na inganta al’umma, suna kuma yi hakan ne ta hanyar bada gudunmawa ta kudade da kuma kayayyakin aiki wadanda suk esamu daga mambobinsu, su yi wadansu ayyukan da su gwamnatocin su ya kamata su yi, wannan ya nuna ke nan suna taimakawa wajen hanyar taimakon kai da kai, saboda kuwa ayyukan sau da yawa sune suke amfana dasu, don haka ma ana iya cewar abin kamar yi wa kai ne, domin ai dama yin noma yana hana yin awo wato sayen kayayyakin abinci, hakanan ma idan su suka bada yawancin kayayyakin da al’umma suka taimakawa kansu, sun fi kulawa dasu fiye da ace gwamnati ce ta sa kudadenta kacokam wajen aiwatar da ayyukan.
Shekarun baya kungiyoyin kulob kulob sun bada muhimmiyar gudunmawa, da kuma taka rawa, wajen ci gaban duk wuraren da suke zaune, wajen aiwatar da ayyukan da zasu inganta rayuwar al’ummarsu. Ga wadanda suka sani a lokacin da kungiyoyin suke cikin ganiyar su sosai da sosai, akwai sashen kula da jin dadin jama’a wanda yana karkashin ko wacce Karamar Hukuma ne a lokaci, sashen ne kuma ya ke taimakawa su kungiyoyin ‘yan kulob din wajen aiwatar da ayyukan ci gaba. Yanzu halin da ake ciki su wadannan kungiyoyi ku san, kamar ana iya cewa sun yi dogon barci mai nauyi, idan aka tuna da irin namijin kokarin da suka yi wajen bada tasu gudunmawar, kusan hakan ne ma za a iya cewar yasa al’amuran ci gaba suka ja da baya, musamman ma a Arewacin Nijeriya wurin da shike da yawan su kungiyoyin kulob kulob a Nijeriya. Idan da ace su kungiyoyin kulob kulob suna nan kamar yadda suke yadda kowa ya san su a da, ai da halin da aka shiga yanzu na ta barbarewar ayyukan ci gaban al’umma, da ba a kawo ga halin da ake ciki yanzu ba. Kungiyoyin kulob da kuma gwamnatoci kamar danjuma ne da kuma dan jummai, saboda abokan junane wajen taimakon juna wanda daga karshe dukkansu kowa zai kasance cikin annashuwa. Hannu daya baya daukar jinka saboda haka akwai bukatar su gwamnatoci su rika taimaka masu, wajen kokarin da suke na inganta rayuwar al’umma na Karkarkar da kuma cikin Birni, wajen taimaka masu yadda za rika kula da ayyukan da aka yi, saboda a dade ana cin moriyarsu, ba wai kuma dan kan kankanen lokaci kuma ace sun lalace. Domin kuwa akwai halin ko in kula wanda wasu mutane ke nunawa, koda ma ace sun fara lalacewar, sai kaga wasu wuraren ma taruwa ake wajen taron dangi na karasa su, ba wanda ya damu kowa ma ya rasa, al’amarin da kuma nan gaba sai an yi dana sani wanda keyace saboda ai a baya take. Koda yake dai idan an bi ta barawo sai kuma abi mabi sawu saboda suma gwamnatocin wasu lokutta da akwai laifinsu, ta wajen nuna halin ko in kula dangane da ayyukansu, wanda sam bai kamata su yi hakan ba. Idan dai har za ayi ma wasu ayyukan ci gaban kansu, ashe kuwa wannan ya nuna ke nan su, al’ummar da suke zaune wuraren da aka yin ayyukan su ya kamata su lutra da ayyukan, saboda ba don komai ba kowa rai ya yi ma dadi to baran mai shi ne.
Gwamnatoci ya dai dace da su farfado da kungiyoyin ‘yan kulob kulob saboda suna taka muhimmiyar gudunmawa, wajen taimakon kai da kai, wadan da suma gwamnatocin sun kwana da sanin cewar kungiyoyin suna taimaka masu ne.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Chelsea Ta Kori Antonio Conte

Next Post

Yadda Hausawa Ke Neman Aure A Zamanin Jiya Da Kuma Zamanin Yau

Labarai Masu Nasaba

Messi

Har Yanzu Messi Ya Fi Kowa Daukar Albashi A Tamaula

by Abba Ibrahim Wada
2 days ago
0

...

An Yi Lugudan Wuta Ta Jiragen Yaki Kan Isis An Kashe Kwamandanta Bin-umar A Tabkin Chadi

Dakarun MNJTF Sun Yi Barin Wuta Kan ‘Yan Boko Haram Sun Kashe 300 A Tafkin Chadi

by Leadership Hausa
6 days ago
0

...

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

...

Ramadan: Diyar Marigayi Sheikh Ja’afar Ta Fara Tafsirin Al-qur’ani A Masallacinsa Da Ke Kano

An Kashe Mutum 172, An Yi Garkuwa Da 23 A Arewa Maso Gabashin Nijeriya Cikin Watanni 3 —Rahoto

by Leadership Hausa
2 weeks ago
0

...

Next Post
Yadda Hausawa Ke Neman Aure A Zamanin Jiya Da Kuma  Zamanin Yau

Yadda Hausawa Ke Neman Aure A Zamanin Jiya Da Kuma Zamanin Yau

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: