Jam’iyyar PDP ta soke taron yakin neman zabenta na shugaban kasa a jihar Ribas da ta shirya yi a ranar Talata 14 ga Fabrairu, 2023, sakamakon yawaitar hare-haren da ake kaiwa mambobinta da magoya bayan dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Fatakwal a ranar Litinin, shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar, Sanata Lee Maeba, ya ce tuni Gwamna Nyesom Ezenwo Wike ya ayyana magoya bayan Atiku a jihar a matsayin makiyan jihar.
Maeba ya bayyana cewa, magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar na fuskantar hare-hare iri-iri daban-daban wanda ke barazana ga rayuwarsu tun daga watan Mayun 2022 lokacin da Wike ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a hannun Atiku.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp