Wasu mayakan Boko Haram da ke tserewa harin bama-bamai da sojoji suke kai musu a jihar Borno, mayakan kungiyar ISWAP dake yankin suma sun kara farmakarsu.
Hare-haren sojoji kan masu tada kayar baya a yankin tafkin Chadi ya ta’azzara a ‘yan kwanakin nan.
A baya dai mun rahoto muku yadda aka kashe mayakan Boko Haram sama da 200 da kwamandojinsu a wani farmaki da sojoji suka kai musu da kuma yadda ambaliyar ruwa ke kara fatattakar maharan wacce ta tilasta musu sauya sheka zuwa gabashin karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.
Wasu daga cikin wadanda suka tsere suka nemi mafaka a kauyen Cina da ke karamar hukumar Bama a jihar amma sai abokan hamayyarsu (ISWAP) suka sake kai musu farmaki kamar yadda majiya ta bayyana.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya ce hare-haren da sojojin suke kai wa ya tilasta wa daruruwan ‘yan ta’adda da iyalansu barin sansanoninsu domin neman mafaka a wasu wurare.
A makwannin baya-bayan nan Dakarun Bataliya ta musamman ta 199, bataliya ta 222, da hadin gwiwar dakarun farar hula tare da hadin gwiwar rundunar sojojin sama, sun kashe mahara akalla 250.