Wani jirigin sama mai saukar Ungulu da ke dauke da shugaban bankin Access, Herbert Wigwe da wasu mutane biyar, ya yi hatsari a Jihar California ta Amurka, kuma duka Fasinjojinsa sun rasu.
Majiyoyi sun ce, jirgin ya nufi Las Vegas ne lokacin da ya faɗo kusa da wani gari mai iyaka tsakanin Nevada da California a daren Juma’a.
- OPEC Ta Samar Da Dala Biliyan 1.7 Don Bunkasa Wutar Lantarki A Afirka
- Yadda Majalisar Wakilai Ta Gana Da Gwamnan Babban Banki Da Ministan Kudi A Kan Matsalar Tattalin Arziki
Wigwe da matarsa da ɗansa suna cikin jirgin da ya yi hatsari ya faɗo a California kusa da iyakar Nevada.
Fasinjoji shida ne a cikin jirgin kuma babu wanda ya tsira. Gwamnatin Amurka ta tabbatar da mutuwar dukkan mutanen da ke cikin jirgin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp