Shugaba Bola Tinubu ya nada tsoffin gwamnonin jihohin Ribas da Ebonyi, Nyesom Wike da Dave Umahi a matsayin ministocin babban birnin tarayya Abuja da kuma ministan ayyuka.
Shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru a matsayin ministar tsaro, da Hannatu Musawa a matsayin ministar fasaha, al’adu da kere-kere.
Sauran sun hada da Lateef Fagbemi, SAN a matsayin ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, yayin da tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya zama ministan sufuri.
Har ila yau, an kebe ma’aikatar Muhalli da kula da yanayi ga Jihar Kaduna, wanda kawo yanzu babu wanda aka zaba daga Jihar.
Ga cikakken jerin Ministocin da ma’aikatunsu:
- Ministar Fasaha, Al’adu da kere-kere – Hannatu Musawa
- Ministan tsaro – Muhammad Badaru
- Karamin Ministan Tsaro – Bello Matawalle
- Karamin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sunumu
- Ministan gidaje da raya birane – Ahmed Dangiwa
- Karamin Ministan gidaje da raya birane – Abdullahi Gwarzo
- Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki – Atiku Bagudu
- Ministan Muhalli da yanayi – Kaduna
- karamin Ministan babban birnin tarayya, FCT – Mairiga Mahmud
- Karamin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli – Bello Goronyo
- Ministan Noma da tanadin abinci – Abubakar Kyari
- Ministan Ilimi – Tahir Momoh
- Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’idu Alkali
- Ministan Harkokin Waje – Yusuf Tuggar
- Ministan Lafiya da ci gaban Jama’a – Ali Pate
- Ministan harkokin ‘yan sanda – Ibrahim Gaidam
- Ministan Ma’adinai – Umar Maigari Ahmadu
- Karamin Ministan Ma’adinai – Shuaibu Audu
- Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a – Muhammed Idris
- Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a – SAN, Lateef Fagbemi
- Ministan Kwadago da samar da Aiki – Simon Lalong
- Karamin Ministan harkokin ‘yansanda – Iman Suleiman Ibrahim
- Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci – Zephianiah Jisalo
- Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli – Joseph Utsev
- Karamin Ministan Noma da Tanadin Abinci – Aliyu Sabi Abdullah
- Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya – Festus Keyamo
- Ministan Matasa – Abubakar Momoh
- Ministar Harkokin jinkai, Agajin gaggawa da Rage Radadin Talauci – Betta Edu
- Karamin Ministan Albarkatun Gas – Ekperikpe Ekpo
- Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur – Heineken Lokpobiri
- Ministan raya wasanni – John Enoh
- Ministan Babban birnin tarayya- Nyesom Wike