Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a yammacin Larabar nan ya isa Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, domin ganawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.Taron bai rasa nasaba da neman takarar shugaban kasa na Tinubu da kuma bukatar samun amincewar Obasanjo gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
- Babu Wata Matsala Tsakanina Da Shekarau —Kwankwaso
- Tinubu Bai Cancanci Zama Shugaban Kasa Ba, Ya Tsufa, Cewar Surukinsa Tee Mac
Tinubu, wanda ya isa gidan tsohon shugaban kasar Penthouse da ke cikin harabar dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), Òkè – Mosan, Abeokuta da misalin karfe 1:00 na rana, ya samu rakiyar kakakin majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila da Cif Bisi Akande da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu.
Magoya bayansa da ‘yan jam’iyyar sun tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Gwamnan jihar, Prince Dapo Abiodun, da wasu tsoffin gwamnonin jihar guda biyu, Àrèmo ‘Segun Osoba da Gbenga Daniel, sun tarbe shi tare da wasu jami’an gwamnatin jihar.
Daga nan kuma tinubun ya shiga ganawar sirri da Obasanjo, ana sa ran zai yi jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC da ‘yan jam’iyyar a filin wasa na Moshood Abiola International Stadium da ke Abeokuta.