Wasu da ake kyautata zaton ‘Yan bindiga ne a ranar Lahadi, sun yi garkuwa da kwamishinan gidaje da raya birane na jihar Benue, Cif Ekpe Ogbu, da wasu mutane uku.
Wata sanarwa dauke da sa hannun dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Ado Oriri Ocheje Richard a karkashin jam’iyyar SDP ta ce, an yi garkuwa da Ogbu ne tare da Hon. Agbo Ode, daya daga cikin surikansa da direbansa.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama A Wani Masallaci A Katsina
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane A Masallaci A Delta
Sanarwar ta ce, an yi garkuwa da su ne a gonar David Mark, bayan Akpa Otobi a lokacin da suke kan hanyarsu daga Otukpo zuwa Utonkon a karamar hukumar Ado ta jihar Benue.
“An ce Kwamishinan ya halarci wani taro a Coci, inda Sanata Abba Moro mai wakiltar mazabar Benuwe ta Kudu ya yi wani taro kan takararsa ta majalisa da kuma yakin neman zabensa a cocin St. Augustine Catholic Church, Otukpo.
“Bayan ya kammala taron, ya je kauyensu da ke Ndekma, gundumar Utonkon a karamar hukumar Ado, kafin ya gamu da mummunan lamarin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, 2022.
“Tun daga lokacin an kwato motarsa daga wurin da lamarin ya faru kuma an kai shi ofishin ‘yan sanda na da ke Otukpo, yayin da duk wayoyinsu aka kashe su,” inji shi.
Kanin kwamishinan jihar Benue, Engr. Tony Ogbu, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwe ya samu labarin garkuwar kuma suna nan suna duba lamarin.
Ya ce tun lokacin da aka yi garkuwa da babban yayansa, har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi ‘yan uwa ba domin neman kudin fansa, inda suka yi addu’ar Allah ya tsare dan uwansa ya kuma dawo da shi lafiya zuwa ga iyalansa.