‘Yan bindigar da suka farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, sun sako ragowar fasinjojin jirgin da ke hannunsu, bayan shafe watanni shida a hannunsu
A wata sanarwa da Farfesa Usman Yusuf, sakataren kwamitin shugaban kasa na mutane bakwai da babban hafsan-hafsoshin sojin kasa, Janar L E O Irabor ya kafa domin sako wadanda lamarin ya rutsa da su, ya ce an sako wadanda harin ya rutsa da su ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Laraba.
- Adron Homes Na Taya Nijeriya Murnar Cika Shekaru 62 Da Samun ‘Yancin Kai
- Dan Majalisar Kano Ya Dauki Malamai 105 Aikin Wucin Gadi
“Na yi farin cikin sanar da al’umma da duniya cewa da misalin 4:00 na yamma a yau Laraba 5-10-2022, kwamitin mutum bakwai na shugaban kasa wanda babban hafsan-hafsoshin soji, Janar L E O Irabor ya kafa, ya tabbatar da sakin sauran fasinjoji 23 da aka yi garkuwa da su.
“Mayakan Boko Haram sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.
“Al’ummar kasa na mika godiyarsu ga sojojin Nijeriya karkashin jagorancin hafsan-hafsoshi wadanda suka jagoranci aikin ceton tun daga farko har karshe. Dukkan Hukumomin Tsaro da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya sun ba da gudummawa sosai ga wannan nasara.
“Tallafin shugaban kasa Muhammadu, ke bayarwa ne ya sanya aka cimma nasara.
“Mambobin wannan kwamiti suna godiya da irin karramawa da alfarmar da aka ba su na kasancewa cikin wannan aikin agaji.
Sanarwar ta kara da cewa “Allah Madaukakin Sarki Ya kara ba mu kariya, Ya kuma kawo mana zaman lafiya a kasarmu.”