A ranar Litinin ne wasu ‘Yan bindiga suka kai hari a hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar Imo da ke Owerri, babban birnin jihar.
Sai dai jami’an ‘yan sandan da ke bakin aiki a wurin sun fatattaki maharan tare da bindige uku daga cikinsu.
Wasu Majiyoyi sun ce maharan sun fara harbe-harbe a wurin ne da misalin karfe biyu na dare tare da jefa abubuwa masu fashewa a cikin gida, lamarin da ya lalata wasu sassan hedikwatar INEC kafin kawo daukin ‘Yan sanda cikin.
An kwato motoci da bindigu da na’urorin sadarwa da dama daga hannun maharan.