Kawo yanzu dai tuni wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Arsenal suka bayyana yadda kociyan kungiyar na yanzu, Mikel Arteta ya kawo gagarumin gyara a kungiyar musamman yadda take buga wasa a wannan lokacin.
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ita ce ta daya inda ta dauki hanyar lashe Premier League na bana karkashin Mikel Arteta, kofin da rabonta da shi tun kakar wasa ta 2003 zuwa 2004.
- Naja’atu: Cikon Banci Ce A Wurinmu, Tun Da Muka Kore Ta Take Ta Sambatu – APC
- 2023: INEC Da ‘Yansanda Sun Nanata Kudirin Samun Sahihin Zabe
Hakan yana nufin Arsenal ta sauya fasali tun daga salon buga wasa zuwa mai kayatarwa da fitar da kudi mai yawa wajen cefanen ‘yan wasa ba kamar yadda aka san kungiyar ba a baya.
A wannan kakar Arsenal tana jan ragamar Premier tana cikin wasannin European Cup da kuma FA Cup a kakar nan kuma wannan ci gaba da Arsenal ta samu ya samo asali daga daukar tsohon dan wasanta, wanda ta bai wa aikin horar da kungiyar ta kuma mara masa baya.
Arsenal ta dauki Mikel Arteta ranar 23 ga watan Disambar shekara ta 2019 daga Manchester City yana mataimakin mai koyar da Pep Guardiola, wanda shima dan asalin kasar Sipaniya ne.
Arsenal ta kammala kakar wasan shekara ta 2018 zuwa 2019 a mataki na takwas, bayan da cutar Korona ta kai tsaiko a gasar da Liberpool ta lashe kofin sannan a kakar
Shekara ta 2020 zuwa 2021 ma Arsenal ta takwas ta kara yi, sakamakon kasa taka rawar gani, kuma wasan farko da Arteta ya fara jan ragama shi ne 1-1 da Bournemouth ranar 26 ga wasan Disambar 2019.
Amma tun daga nan Arteta ya lashe FA Cup a Arsenal da kai kungiyar Europa League, duk da cewar ya fuskanci kalubale a farkon aiki da wasu ke gannin ba zai iya ba a kakar wasan 2021 zuwa 2022.
A wannan kakar ne Arteta ya kare a mataki na biyar, bayan da a wasan karshe abokiyar hamayya Tottenham ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun turai na Champions League.
To sai dai a bana Arsenal ta zama sabuwa, bayan da Arteta ya gama lakantar gasar Premier League ya kuma dora Arsenal kan turbar lashe kofin na bana duk da cewa wasu suna ganin kamar ba zai iya ba.
Arsenal mai kwantan wasa daya ta doke Manchester United ranar Lahadi a gasar Premier League da ci 3-2 – hakan ya sa kungiyar ta ci gaba da jan ragamar teburin gasar.
Dama Manchester United ce kadai ta ci Arsenal 3-1 a gasar Premier League a bana, sai kuma 0-0 da Newcastle United, wanda ba ta zura kwallo a raga ba a wasan haka kuma Arsenal ta tashi 1-1 a gasar Premier League a gidan Southampton.4
Rabon da Arsenal ta dauki Premier League tun kakar 2003 zuwa 2004 karkashin Arsene Wenger kuma cikin wasanni 19 da Arsenal ta buga a kakar nan ta ci 16 da canjaras biyu da rashin nasara daya, wadda take da maki 50.
Haka kuma kungiyar ta ci kwallo 45 aka zura mata 16 a raga, kenan tana da rarar 29 kawo yanzu kuma tun daga lokacin da Arteta ya karbi aikin kociyan Arsenal ya yi wasa 115 a Premier League da cin 65 da canjaras 18 da rashin nasara 32.
Haka kuma tsohon dan wasan na Arsenal ya ja ragamar kungiyar ta ci kwallo 193, sannan aka zura mata 124.
Ranar 9 ga watan Nuwamba Brighton ta fitar da Arsenal daga Carabao Cup da ci 3-1 a filin wasa na Emirates sannan ranar 27 ga watan nan Arsenal za ta fafata da Manchester City a FA Cup, wasan zai zama na hamayya kuma zakaran gwajin dafi ga kungiyar.