Fadar White House ta kasar Amurka ta sanar a kwanan baya cewa, shugaba Joe Biden na kasar Amurka ya jinkirta ziyararsa a kasashen Jamus da Angola, wadda aka tsara yi a tsakiyar watan Oktoban bana, saboda ya mai da hankali kan daidaita yanayin da mahaukaciyar guguwa ta haifar. Yau shekara daya ke nan da Biden ya yi alkawarin ziyartar Angola, amma ya yi ta jinkirta ziyarar sau da dama, lamarin da ya tunatar da mutane yadda Amurka ta lashi takobin taimakawa kasashen Afirka, amma ba ta cika alkawarinta ba sau da dama.
Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya sa hannu kan shirin dokar bunkasar Afirka da samar da damammaki wato AGOA a takaice, wanda ya kara bude kofar Amurka ga Afirka da kuma fadada ba da fifiko ga Afirka. Sai dai kash! ba abincin bati. Sakamakon babban gibin da ke tsakanin Amurka da kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da bunkasar kasa, ya sa shirin dokar AGOA ya sanya Amurka cin ribar fitar hankali, a maimakon ba da fifiko ga Afirka.
- Sin Ta Fitar Da Shirin Bunkasa Ayyukan Kimiyyar Sararin Samaniya Na Shekarar 2024 Zuwa 2050
- Me Ya Sa Ake Iya Kara Yin Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da ASEAN Bisa Yanayin Da Ake Ciki?
Haka kuma, bisa shirin dokar AGOA, kasashen Afirka suna sayar da kayayyaki zuwa tsirarun sana’o’i da kuma tsirarun kasashe. Ba a cimma burinsu na sayar da kayayyaki zuwa kasashe da yawa ba. Har ila yau, shirin dokar ta saukaka tsare-tsaren Amurka na sayen man fetur da iskar gas da wasu muhimman ma’adinai daga Afirka, da fadada sayar da kayan Amurka zuwa Afirka, da kara zuba jari a Afirka ta fuskar makamashi. Ban da wannan kuma, Amurka ta gindaya wasu sharuddan siyasa cikin shirin dokar AGOA, ta kan yi wa kasashen Afirka barazanar soke fifikon ciniki, haka ya dora kasashen Afirka kan matsayi mai rauni.
Yadda Amurka ta yi danniya da cin zalin wasu da sunan zuba jari da ba da taimako, a yunkurin ci gaba da ba da tasiri a Afirka, zai sa ta rasa goyon bayan al’ummar Afirka. (Tasallah Yuan)