Connect with us

LABARAI

Da Sauran Gyara Wajen Farfado Da Noma A Nijeriya – Salisu Mai-Masara

Published

on

An shawarci gwamnatin tarayya musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya sake duba matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na batun bunkasa noma, domin tsarin da aka sa wa gaba, a sami nasarar da ake bukata.

Fitaccen manomin nan da ke garin Soba, a jihar Kaduna mai suna Alhaji Salisu Nuhu Mai Masara Soba ya bayar da shawarar a lokacin da ya zanta da manema labarai a Zariya,jim kadan bayan wata jarida mai suna Taskira ta karrama Magayakin Soba, Alhaji Lawal Umar Auwal, a Zariya.

Alhaji Salisu Mai Masara ya ci gaba da cewar, duk wasu tsare–tsare da za su bunkasa noma, a cewarsa gwamnatin tarayya ta yi tsarin, sai aka manta ba a  cusa ainihin manoma a tsare – tsaren ba, wannan kamar yadda babban manomin ya ce, babbar matsala ce da ya dace tun a shekara daya da fara aiwatar da tsarin gwamnatin tarayya ya dace ta fahimta haka.

Saka manoma a cikin tsare – tsaren bunkasa noma a daukacin Nijeriya, ya na da matukar muhimmanci, kamar yadda ya ce domin in an sa masana sana’ar a gaba, da kuma suka san matsalolin da manoma na gaskiya  ke cik, za a sami biyan bukata a lokaci kadan.Amma cusa wadanda ba su da alaka da noma,  a cikin kwamitin bunkasa noma, babbar matsala ce da ya kamata gwamnatin tarayya ta fahimta, sai aka sami akasin haka, in ji shi.

Sauran matsalolin da suka yi wa batun farfado da noma a Nijeriya hawan kawara su ne na yadda gwamnatin ke bakin kokarinta, amma sai aka wayi gari ‘yan baya ga dangi suna shigo wa da kayayyaki  noma, wannan kamar yadda Alhaji Salisu mai masara ya fshimta, tamkar yi wa gwamnatin tarayya  zagon kasa ne a lamurran gwamnatin tarayya na ciyar da bangaren noma gaba.
Advertisement

labarai