Dan takarar Majalisar Tarayya a Jam’iyyar PDP a Kano Municipal, Yusuf Da’awa, ya kaddamar da taron sanya yara marasa galihu guda 1300 a makaranta da samar musu da kayan makaranta da sauran ababan koyon karatu.
Injiniya Da’awa, ya ce manufar bayar da tallafin shi ne samar da karin masu zuwa makaranta ga yaran da iyayensu ba su da karfin daukar nauyin karatunsu.
- 2023: Sarkin Kano Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bukaci INEC Ta Gudanar Da Sahihin ZabeÂ
- Ana Bukatar Ruwa Lita Miliyan 200 A Kullum A Kano – Kwamishina
A cewar Da’awa, “babu yadda za a magance tarin matsalolin da ke damun al’umarmu ba tare da an samar da wata dama da yara zasu samu ilimi ba, ba tare da la’akari da nauyin aljihun iyayensu ba.”
“Allah ya sani ni dan talakawa ne kuma ina alfahari da damar da Allah ya bani ta taimakawa al’uma, kuma babban buri na shi ne yadda muka hadu anan a ce bayan wasu shekaru an samu wasu daga cikin wadannan yara sun tara wasu yayan talakawa domin daukar nauyin karatunsu, ko da rai na ko babu.”
Daga nan Injiniya Yusuf Abdullahi, wanda shi ne mafi kankantar shekaru cikin jerin ‘yan takara masu neman sahalewar al’umarsu domin su wakilce su a majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya.
“A baya mun dauki nauyin karatun dalibai da dama wajen rubuta jarabawar WAEC da NECO da kuma JAMB tsahon shekaru da suka wuce,”
“Hakan kuwa na da nasaba da nazari da muka yi akan alkaluma da ke nuni da cewa wani kaso mafi tsoka na dalibai kan hakura da ci gaba da karatu saboda gazawa wajen samun kudin wadannan jarabawa, shi yasa muka dukufa wajen ganin cewa mun yi iya yinmu wajen tabbatar da cewa mun tallafi karatun dalibai da dama a fadin wannan karamar hukuma.” Cewar Da’awa.
Da’awa ya kuma kara da cewa nan gaba kadan zai sake kaddamar da shirin koyar da sana’o’in dogaro da kai ga mata da matasa, domin rage radadin tattalin arziki da ake fama da shi.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, akwai tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Ghali Umar Na’abba da jigo a jam’iyyar PDP a nan Kano, Ibrahim Aminu Dan’iya da ma sauran manyan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar birni da dama.