Yahaya Usman Alfadarai" />

Dabarun Noma Waken Suya Na Zamani

Masu karatu barkan mu da saduwa a wannan dandali namu na noma tushen arziki,An ce a sha ruwa akoma aiki, bayan gama hutun sallah yanzu za mu koma aiki, Sanboda haka kamar yadda muka saba za mu kawo muku sakamakon bincike-bincike da cibiyoyi bincike da bunkasa harkokin noma suke gudanar a fadin kasar nan, za mu leka cibiyoyi irin su IITA  da IAR da NAERLS da NAPRIL da Hukumomin bunkasa aikin noma na jihohi, za kuma mu rinka yin tattaki zuwa manya da kananan gonaki da ke fadin kaar nan domin jin yadda masu gudanar da gonakin suke harkokin su da nufin amfanar da masu karatunmu, muna sa ran tattauna da masana a fannoni daban-daban na ikin noma, kofar mu kuma abude ta ke domin karbar shawarwari da gudumma wa abin da zai anfanar da al’ummarmu, tuni dai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nuna aniyarta na ba harkokin noma da kiwo mahinmaci da ya dace. Saboda haka a wanan makon za mu kawo muku bayani ne a kan dabarun noman waken suya.

GABATARWA

Waken suya na daya daga cikin amfanin gona da aka sansu tun da dadewa a can nahiyar ASHIYA (Asia), wanda suke noman sa dan samar da mai da madara da kuma sauran sinadaran kara kuzari irin su PROTEIN da sauran su. A na noman waken suya ne a waje mai yanayin zafi. Ainihin manoman waken suya kamar yadda binciken masana ya nuna suna noman shine don samar da takin gargajiyya sakamakon yawan sinadarin nan na NITROGEN da yake kunshe dashi. Musamman ga manoma masu yin noman kewaye wato (crop rotation) inda ake shuka shi a matacciyar gona bayan ya  fito sai su bi shi da kasa su binne daga baya kuma sai a shuka amfani.

Cigaban da aka samu na fasahar zamani ta hanyar sarrafa da adana man waken suya yasa aka samar da hanyoyin amfani dashi daban-daban, wannan mukala da yardar mai-duka zata tattauna a kan abin da ya shafi tarihi da asali da cigaban da aka samu a duniya wajen noman waken-suya, wannan ya kunshi  nomansa da cututtuka da kwarikan da ke addabarsa da yadda za a magancesu da yadda ake zuba taki da girbinsa da yadda manomi zai adana shi, da kuma uwa-uba yin tsokaci kan irin muhimmiyar gudummawar da waken-suya ke bayarwa wajen cicciba tattalin arzikin duniya.

TAKAITACCEN TARIHI

Kamar yadda muka fada tun da farko, yankin Ashiya (Asia) shi ne yanki na farko kamar yadda masana suka fada da aka fara noman waken-suya, wanda suke noman sa a matsayin dangin furannin dajin nan da ake kira da (Glycine soja) kusan shekara 5000 da suka gabata. Duk da haka, asali da tarihin noman waken-suya ba zai cika ba tare da ambaton wannan shararren jarumin nan na kasar Sin (China) wato SHENNONG wanda akewa lakabi da ‘’DIBINE FARMER’’, masana tarihi sun tabbatar da cewa shi ne wanda ya kawo fasahar noma ga mutanen kasar Sin da kuma Biyatnam (Bietnam), ance ya sanya waken-suya a cikin furannin daya kira ‘’Tsarkakakkun furanni guda biyar’’ wanda suka kunshi shinkafa da alkama da dawa da kuma gero. Haka nan a shekara ta 1000 kafin haihuwar Annabi Isa aka fara noman waken-suya a kasar Jafan (Japan) da Koriya (Korea) wato tun  a zamanin mulkin Rumawa.

Waken-suya yana daga cikin dangin Legum wanda ya hada da wake da sauran su. Wannan dangi shi ne na uku mafi girma a dangin furannin kallo, dake dauke da dangi kala-kala har kusan 15,000. Waken-suya a kewaye yake yana dauke da launin ruwan dorawa-dorawa. Saboda yawan maikon da yake dashi da kuma sinadarin PROTEIN daya kunsa yasa a kan iya sarrafa waken-suya ta hanyoyi daban-daban domin amfani iri-iri.

Masana tarihi sun tabbatar da cewa noman waken-suya ya bulla a nahiyar turai da kasar Amurka tun a lokacin mulkin mallaka. Haka nan manoman yankin Ashiya sun fara noman waken-suya ne ka’in da na’in a shekarar 1910. Tun daga sannan noman waken-suya ya habbaka a wannan yanki, inda a halin yanzu kasar Amurka ke jagoranta da kashi 55 cikin dari wato (55%) yayin da idan muka dawo yankin mu na Afirika kuma kasarmu ce ta Najeriyya ke jagoranta yayin da kasar Afirika ta kudu (South-africa) ke rufa mata baya.

WAKEN-SUYA:TAKI

Adadin yawan takin  da gona ke bukata domin noman waken-suya ya ta’allaka da irin dandanan kasar da kuma yankin da gonar take.  Kamar yadda mu ka yi tsokaci a baya kuma akasarin manoman waken-suya suka sani cewar waken-suya baya bukatar takin da ke kunshe da sinadarin NITROGEN kasancewar da kansa yake samarwa kansa wannan sinadari, kuma kamar yadda binciken masana kimiyyar noma ya nuna waken-suya na  dogara ne  kacokan  da sinadarin NITROGEN domin girma. Binciken kuma ya tabbatar da karancin sinadarin PHOSPHURUS a waken-suya  don haka ake bukatar manomi da ya zuba taki mai dauke da wannan sinadari na PHOSPHURUS domin samun amfani mai yado.  Ana bukatar manomi ya zuba  sinadarin PHOSPHUROS da ya kai adadin kilo 30  a duk kadada guda (hecter)  ta hanyar amfani da takin da ake kira da  (super phosphate fertiliser).  Hakanan taki mai dauke da sinadarin NITROGEN da POTASSIUM  ana zuba sune kawai a yayin da manomi ya fahimci  karancin su kuru-kuru a cikin gona.  A kan iya cakuda  takin  da a ke son amfani  da shi  yayin yin  sharar gona ko  lokacin yin haro (Harrow).

NOMAN WAKEN-SUYA: TAGOMASHI

Kamar yadda  muka fada  a baya waken-suya  na kara tagomashin  gona ta hanyar sanya adadi mai yawa da  gona ke bukata na sinadarin  NITROGEN a cikin kasa.  Musamman ma idan manomi ya shuka shi tare da masara yana taimakawa gaya wajen kashe muguwar  ciyawar nan da ake kira da   stringa hermonthinca.

Kwarirrika da cututtukan da ke addabar waken-suya da hanyoyin magance su a gona.

Ciyayi da yadda za a magancesu

Ciyayin dake addabar waken-suya duk shekara ko kuma a shekara sau biyu , wato lokacin noman damina da kuma lokacin noman rani , sun fi addabar waken-suya yayin da ya yi tsiro ya dan fara girma. Don haka tashi tsaye ga manomi a kan lokaci domin magance wannan matsala kan iya rage karfi da kuma tasirinta a jikin waken-suya. Manomi kan iya magance tasirin ciyayi a  cikin gona ta yin amfani da hanyoyi guda biyu da zamu ambata, wato ko dai ta yin amfani da  hanyar gargajiyya ko kuma ta yin amfani da hanyar zamani.

HANYAR GARGAJIYYA; a nan ana bukatar manomi ya fara nome ciyayin da suka fito a  cikin gona sati biyu bayan shuka, sannan sai ya bari sai bayan sati na biyar zuwa shida da yin shuka ya kara yin wata nomar. Yana da kyau manomi ya kiyaye  yin gaggawa wajen yin noman ciyayin gona tun kafin ruwan sama ya kan-kama domin yin hakan zai iya zama yin aikin baban giwa. Hakanan yin noman ciyawa mara kyau ko kuma dogon jinkiri wajen nome ciyayi zai iya rage yawan amfanin da za a samu in an zo girbin waken-suya.

Hanyar Zamani; a nan ana bukatar manomi ya yi amfani da  magungunan feshi don kashe ciyayin da suka fito yayin noman waken-suya. Magungunan  feshin  ciyayi suna da tasiri sosai in manomi yayi  amfani dasu yadda ya kamata.  Kazalika zaben magani kashe kwari daya  kamata manomi yai amfani dashi  a cikin gonar sa ya ta’allaka da iri yanayi ciyawar da ta fito da kuma saukin samun maganin a inda manomin yake.  Duk da cewa magungunan kashe ciyayi suna nan a wadace, ga ciyayin da basu bayyana ba dama wadanda suka bayyana   a cikin gona.  Don haka in aka fesa maganin kashe ciyayi  a cikin gona,  manomi zai fara nome ciyawa da zarar an shiga sati na biyar zuwa shida da shuka.

 

Exit mobile version