Connect with us

NOMA

Dabarun Noman Albasa

Published

on

07084634387 09096984945

NAERLS/ABU ZARIA Samaru Zariya

Gabatarwa

Albasa na daya daga cikin muhimman abinci na yau da kullum a kasashen Afrika wajen gyara miya, sannan kuma ga saurin kawo naira.

A Nijeriya an fi nomata a jihohin Arewa, kuma a kan nomata rani da damina.

Zaben Wuri

Zabi wuri mai ni’ima mai isasshen taki wanda baya cin ruwa, kuma marar duwatsu ko marmara.

 • A lokacin rani sai a zabi bakin fadama ko kusa da rafi ko kogi ko madatsun ruwa don samun ruwa.

Zaben Iri

Akwai “Wuyan Bijimi”, da “Jar Albasa”, zabi nagartaccen irin da ya dace da karkarar ku. Tuntubi baturen gona ko Director AERLS/ABU Zaria don shawara.

Gyaran Wurin yafi Iri

 • Zabi wurin da ya dace. Yi kaftu da bubbuge bangarorin kasar ka gyara ya yi lebur.
 • Shirya bedi mai matsakaicin fadi (mita 1 – 1 1/2) mai isasshen tsawo ( ya yi tudu da damina, amma ya yi kwari da rani).

Yafin irin albasa

 • Ja layuka inda za ka yafa irin. Kada zurfinsa ya wuce centimita 1.3 kuma tsakanin layi da layi kada ya wuce centimita 10 zuwa 15.
 • Samo yashi ka cude irin sannan ka yi yafin ko kuma kana iya yin yafin sannan ka barbada yashin, bisanshi.
 • Lullube kan yafin da ciyawa sannan ka yi ban ruwa
 • Idan sabon tsiron ya fito sai a cire ciyawar
 • Idan ka ga sabon tsiro ba ya girma kamar yadda a ke so to sai ka kara masa taki kamar haka:

Auna takin CAN cikin fankon ashana 11 ka zuba cikin ruwa gallon daya  ka dama, har ya narke. Daga nan sai ka malala ruwan a fili mai murabba’in fadin mita biyu.

 • Sabon tsiro zai is a dashe bayan sati 6 zuwa 8 da yin yafi, ko idan ya kai tsawon centimita 15 zuwa 23.

Gyaran Wurin Dashen Albasa

Yi kaftu ka zuba isasshen takin dabbobi (FYM) ko buhu 2 1/2 na supa ga kowace hekta.

 • Idan da rani ne sai ka shirya kunyoyi masu dan bisa wadanda za a rinka yin ban ruwa ta kwarinsu, ko kuma a shirya fangaloli masu zurfi wadanda za su iya ajiye ruwa, kuma a yi ban ruwa ta cikinsu.
 • Da damina kuma sai a yi fangaloli masu tudu (dan bisa)
 • Akan noma Albasa har sau uku a shekara a jihohin Arewa wato farko da karshen damina da kuma lokacin rani. Ga karin bayani:

Fasalin Shuka

 1. Albasa ta farko, lokacin yafin irinta karshen watan Afrilu, lokacin yin dashe tsakiyan watan Yuni, lokaci diba cikin Agusta ko satunba.
 2. Albasa ta biyu, lokacin yafin iri cikin watan june, lokacin yin dashe July zuwa August, lokacin diba Nobember ko December
 3. Albasa ta uku lokacin yin yafi September zuwa December, lokacin yin dashe Nobember zuwa December, lokacin diba March zuwa April.

Yin Dashe A Gona

 • Tugo yabanyar da lura ka dasa daidai zurfin yanda ka cirota. Kana iya rage tsawon ganyayen zuwa centimita 10 idan har sunyi tsayi.
 • Yi dashen kan layuka masu nisan tsakanin centimita 15, nisan tushe da tushe centimita 15.

Karin Taki

Bayan takin da aka sa lokacin gyaran fili, akan so kuma a yi karin takin CAN buhu 5 ga kowacce hekta. Ga yadda za ka yi:

Yi ga naka da buhu 2 1/2 bayan mako 2 ko 3 da yin dashe, sai kuma ka kara wadansu buhu 2 1/2 bayan sati 4 da sawan farko.

Ga Shawara

 • Ka yawaita yin noma, amma ka yi da yar karamar fartanya.
 • Kada karufe duk kwayar albasar da ka gani a waje da kasa. Yin hakan zai sa Albasar ta rube.
 • A lokacin rani sai a yawaita ban ruwa. Yi sau biyu ko uku ya wadatar bisa ga yanayin kasa.
 • Amma a yi hattara. Yawan ruwa ga albasa ya kan sa ta rube.

Kulawa Da Lafiyar Albasa

Kwari da Tsutsotsi Da Cuce-Cuce

 1. Kwari da Tsutsotsi

(a) Tsanya (Gyare) yakan yi barna ga Albasa tun a bedi da bayan an yi dashe. Ga magani. Cuda 1/2 kilo, na maganin Agrocide, da kilo 45 1/2 na dusa ka zuba a kan bedin ko a gonar don gyaran ya ci.

(b) Kwarin Albasa (Onion thrips)

Wadannan kwari ne masu zama kan ganyen Albasa suna tsotse ruwan jikinsa har ya yankwane, ya lalace.

Maganinsu

(I) Idan an gansu (sati 4 zuwa 8 da yin dashe) sai a yi feshi sau uku da maganin cymbushi U.L.B. lita 2 1/2 ga kowace hekta a kowane sati har sai sun mutu.

(ii) Ko kuma a yi amfani da kilo 1.32 na Betod 85 cikin ruwa lita 110 ga kowace hekta.

 1. Cuce-Cuce

(a) Ciwon ganye (Purple blotch)

Wannan ciwon wadansu kananan kwayoyin cutuka na ‘fungus’ ne ke kawo shi. Kuma ciwo ne na rani da damina ya kan sa ganyen Albasa ya yi fari-fari, sannan sai ya canza kasa-kasa nan da nan da zaran yanayin dumi ya samu. Idan abin ya yi tsanani, sai launin ya zama garura – garura. Daga nan sai ganyen ya lakube, ya zama rawaya ya mutu.

Yadda Za A yi Maganinsa

A lura da canjin wurin shuka

A yi amfani da maganin Dithane M45 kuma a rinka yin dashe da wuri

(b) Rubewar Albasa

Ciwone wanda wasu kananan kwayoyin cutuka na hunhuna ke kawo shi. Yakan kama Albasa tun a gona har ya zuwa sito wurin ajiya.

Alamomin kamuwa sune ‘kambori’ a saman ganyayen Albasa da rubewar saiwoyi. A kasan kwayar Albasan kuma za a ga farin hunhuna a sashen da ya rube.

Maganinsa

A yawaita canjin wurin shuka. A tuge duk tushen da ya harbu a binne. A rinka yin dashe a wurin da ruwa baya kwantawa. Kada a yi amfani da takin da bai rube ba. Kada a zuba ruwa ya wuce misali in an zo yin ban ruwa.

(c) Murdewar Ganye

Alamun wannan ciwo shine murdewar ganyen Albasa. Idan ya tsananta kwayar Albasa takan kankance ko ta ksance babu sai dogon tsiro. Wannan cuta ta fi yawa ga Albasar damina.

Maganinta

Dama 1/2 kilo na Benlate da ruwa lita 500 ka fesa ga kowacce hecta. Ko kuma ka dama 1/2 kilo na Benlate da 1/4 – 3/4 na Antracol da ruwa lita 500 ka fesa ga kowacce hekta.

A fara yin feshin kafin cutar ta tsananta, kuma a yi ta yi bayan kowanne mako.

Cirar Albasa

Albasa ta kan isa cira idan mafi yawan ganyayenta sun bushe ko sun zama rawaya. Cire ta da hannu sannan ka kwantar da Albasar ta gefe har misalin kwanaki biyu domin ta tsane ta bushe. Daga nan sai ka kwaso ta ka tara ta a cikin inuwa har na kwana 7 – 14. Sannan sai a yanke ganyen a bar dan guntu kamar dan yatsa (3 – 5 cm) daga nan sai a zabi kwayoyi masu kyau daga kanana da rubabbu.

Ajiyar Albasa

Kwayoyin Albasa masu matsakaicin girma da fadi kawai ya kamata a ajiye. Kada ka ajiye wadanda suka fara yin fure da wadanda basu kosa ba, da kuma manya ainun. Kada ka ajiye kwayar Albasar a kasa. Ajiyeta kan wani abu domin iska ta samu damar ratsawa.

* Ka rinka bi kana tsince duka Albasar da ta rube ko wanda ta fara tsira bayan kowane sati biyu.

* kana iya yin amfani da maganin maleic hydrazide don hana tsirar Albasa a sito.

Tanadin Irin Albasa

Ka da ka yi iri daga Albasar da ta yi fure a shukar farko. Irin da aka samu daga wannan Albasar ba ya jure ajiya kuma yana da saurin ruba.

Ya fi kyau a yi shukar iri dabam a lokacin rani. Ga yadda za ka yi.

* Zabi kwayar Albasa matsakaiciya mai kyau wanda bata taba yin hure ba, kuma wanda ta yi misalin wata 5 – 7 a ajiye.

* sai ka yanke ta a kwance gida biyu ka shuka bangaren kasan (wato gindin) a kan bedi mai isasshen takin gargajiya.

* Ci gaba da yin ban ruwa misalin sati uku har ya tsiro.

* Bayan mako 5 – 6, sabon tsiran tsawonsa zai kai misalin sentimita 15 – 20. Daga nan sai ka rarraba su ka dasa cikin bedi kan layuka masu nisa sentimita 20 nisan tushe sentimita goma goma.

* Yawan tsiron da akan samu daga kwayan Albasa ya danganta ga girmansa ko fadinsa. Amma akan sami 7 ga kanana, 10 ga matsakaita, 20 ga manyan kwaya.

A maimakon wannan hanyar da muka ambata a sama ta samun iri, kana kuma iya shuka kwayan gudan Albasar cikin bedi kan layuka masu nisan tsakanin sentimita 25, nisan rami da rami sentimita 25.

 
Advertisement

labarai