Duk inda ka ratsa a cikin garin Kano baburan adaidaita sahu ko Babura masu ƙafafuwa uku za ka yi ta ganin an rubuta Ja’e zance ya yi ta zagayawa na neman wai wa ye Ja’en nan mace ko namiji? Wa ke da wannan nasibin cikin ƙankanin lokaci haka? amsar na nan tafe a hirar mu da mamallakiyar kamfanin Ja’e Transport
TARIHINTA
Hajiya Aisha Muhammad Ja’e an haife ta a Kawo da ke Kaduna gidan limamin Kawo a shekarar 1967. Ta fara makarantar allo lokacin da na tasa. An yi mata aure tana da shekara goma sha biyu inda a lokacin mijinta yana karatu a CAS da ke Kano, ita kuma tana Kaduna da iyayen miji. Bayan sun dawo Kano tana ‘yar shekara ishirin da biyar lokacin ko baƙi ba ta sani ba a boko sai maigidanta ya saka ta a makarantar boko ta yaƙi da jahilci da ke Library a Kano. A lokacin tana da yara huɗu. Alhamdulillahi a nan ta yi firamare ta gama ta shiga sakandare. Daga aji uku ta daina zuwa kuma dai-dai gwargwado tana iya karantawa ta rubuta. Yanzu haka tana da shekara 38 da aure tare da yara biyar.
FAƊI TASHIN RAYUWA
Haka ta ci gaba da sana’oin gida har zuwa lokacin da Maigidanta ya kammala karatunsa na jami’a ya zama ya zama cikekken lauya. Dawowarsu Kano sai ya zo mata da wani sabon ƙalubalen don a lokacin tana Kaduna tana yin sana’oi daban-daban yanzu kuwa ta dawo Kano sabon waje ba wanda ya santa. A lokacin tana Kaduna tana yin alewar madara irin wadda ake sa wa a leda don haka sai ta yi tunanin ko za a saya in ta yi? Abu kamar wasa sai ta fara yin alawar Madara wanda ita ta fara yin ta a Kano irin wadda ake sayarwa a tituna. Ta fara da kwalin madara Nido guda ɗaya har ta kai kullum sai ta tuƙa katan uku na madara kuma ta ƙare tsakanin masu sari da masu sayen ɗai-dai. Haka ta haɗa da renting na kaset ɗin wasan kwaikwayo na Hausa. Sannan tana sayar da kankara ta yara ta kwalaba da ta madara da ta zoɓo da sauransu ana kai wa makarantar da’awa ana sayar mata da shi.
Da ta ga ɗan kuɗi a hannu sai ta saro atamfa ta dubu daya da ɗari biyar ta bayar a biya ta biya biyu daga nan sai ta saro ɗankwali da mayafi wannan shi ne mafarin shiga harkar kayan sutura da zuwa yau take sayar da atamfa sufa da lesissika shaddoji tana ɗinka na maza da na mata ta kai Saudiyya.
Ta fara harkar sufuri da ta fara yarinyarta da take mata tallan waina da miya wadda a yanzu ita ma lauya ce a lokacin aurenta a 2002 a kuɗin da aka haɗa mata na gudummawa su ne ta haɗa na sayi acaɓa. Duk da a lokacin ana haɗa balance ne sai take ta samun matsala ganin haka sai ta shiga dashi. Da ta ɗau dashin sai ta sai wani babur ɗin amma parchase. A sannu ta ci gaba da harkar babura har zuwa lokacin da aka hana acaɓa a Kano a lokacin tana da babura ɗari biyar a shekarar 2013.
Lokacin da adaidaita ya shigo ta so haɗa babur da adaidaita sai ya zamana Maigidan ya nuna kada a yi don haka sai ta haƙura ta ci gaba da acaɓan kawai. Dalilin komawarta harkar sufurin babur mai ƙafa uku kuwa ta shiga a daidaita sahu suna hira sai mai adaidaitan ya yi mata tallan babur din ko za ta saya. Sai ta ce to za ta yi shawara da Maigidan. Bayan ta tambayi maigidan ya amince sai ta nemi ɗan adaidaitan suka yi ciniki ta saya a ka ci gaba da aiki. Ganin tana yi ƙawarta da yarinyarta da maigidanta da ɗan ƙawarta duk suka kawo nasu ta haɗada nata duk ta kuma ƙara danƙa a hannun wannan wanda ya yi mata talla.
A shekarar 2014sai da ta haɗa a daidaita goma sha uku a hannunsa. Wannan shi ne mafarin shiga harkar adaidaita sahunta. Tana tsaka da harkar wannan wanda yake kula da adaidaita sahun ya gudu gaba ɗaya da baburan sai guda ɗaya ne ya tsira shi ma saboda da hannunta ta ba wa mai hayar.
Bayan an gama bikin autarta sai ta sayi wani babur ɗin ta haɗa da na farko ta kuma shiga dashi a lokacin sai ta sake dabara ta sami yaro wanda shi ke shigar da duk wanda ya kawo balance.
A shekarar 2015 kamfanin a yanzu yana da shekara ɗaya da wata takwas an buɗe kamfanin da adaidaita goma sha huɗu tare da ma’aikata huɗu. Amma a yau ma’aikatanta mutum saba’in da biyar manya hamsin da yara ishirin da biyar. Su yaran ana koya musu harkar makanikanci da juye. Akwai waɗanda suke zuwa da safe in sun tashi sai na yamma su karɓi aikin. dukkansu ana biyansu duk sati. Waɗannan ma’aikata ne kawai na kamfani ba direbobi ba. Sannan duk wannan ma’aikatan suna cin abinci kullum a kamfani.
Bayan harkar adaidaita tana da gidan cin abinci Nini fast food restaurant inda takan leƙa wajen da daddare. Haka Hajiya tana taɓa harkar fina-finan Hausa inda take daukar nauyi a yi aikinsu amma sai ta ɗora ribarta ta sayar bayan an gama aikin ko kuma ma tun ana aikin don haka aikin ba ya fita da sunanta. Misali a kwai fim ɗin Ƙugiya da Ikram da da Madafa da Sirrin ruhi da Niƙab.
ƘALUBALE
Ba wata harkar da mutum zai yi bai gamu da ƙalubale ba ta ko’ina musamman ma a wajen mu mata. Harkar sufuri maza ke yi dole sai an kai zuciya nesa. Babban ƙalubale na farko da ta fuskanta shi ne yadda mutum guda da ka amincewa ka damƙa masa amanar dukiya ya gudu wanda har zuwa yanzu bai dawo ko ta kan iyalansa ba wanda a ƙarshe da muka je kotu rantsuwa ta raba mu. Sai ma ya zamana ita ke taimaka musu da abin da za su ci.
Ko a jiya an zo mata da ƙorafin an sace babur ɗin a hannun wani. Irin wannan satar ana samunta lokaci zuwa lokaci. Wani lokacin an taɓa sace guda uku a sati ɗaya.
DALILAN NASARA
Dalilin nasara na farko dai tana ganin kome daga gun Allah yake yadda ya so haka yake tabbata. Sai abu na biyu maigidanta wanda shi ne ƙashin bayan nasararta duk abinda ta faɗa masa indai ya san na ƙaruwa ne yana ba ta goyon baya bilhasali ma shi ne lauyan kamfanin .
Sai tsari wanda ya taimakawa kamfanin wajen samun nasara. Kome na kamfani a tsare yake suna rufe gate na karɓar balance kullum ƙarfe biyar duk wanda ya zo bayan biyar zai tarar rufe gate kuma sai an ci tarar sa. Da wannan kuɗin tarar ake yin ƙananan aikace-aikacen ofis.
Sannan akwai accountant wanda shi yake karɓar balance a shigar duk sati. Duk wanda bai balance ba a ranar da yake yi za a sanar da ita kuma sai an ci shi tara.
A wajenta ake yin juye da gyara don tana da spare part na duk abin da ake nema ga makanikan kamfani , don haka in abin hawa ya sami matsala za a raba kuɗin gyaran uku kashi ɗaya a ɗauka a balance din , ragowar kashi biyun a biya kamfani a hankula duk lokacin da aka sami sarari. Sun yi haka ne don daƙile kai wa gyara gurin waɗanda ba su iya ba.
Juye ma duk sati ake yi a kamfani an tanadi duk kayan aikin ba ta yarda a je waje a yi ba.
Duk direbobinta tana sama musu sojan haya wanda za su yi aikin tare gudun kada a ba wa wanda ba ta yarda da tuƙinsa ba a ja mata abin hawa.
BURI
Babban burin da ta sa a gaba yanzu shi ne ta buɗe makarantar koyon tuƙin adaidaita sahu da koyon mota don wannan tuni shiri ya yi nisa kan hakan. Babban burinta na ƙarshe shi ne a ga Ja’e Airlanes tana faɗawa yaranta ko da kuwa ba ta da rai su cika mata burinta.
Tare Da Bilkisu Yusif Ali