A wannan watan, shekaru saba’in da biyar da suka wuce, gagarumin al’amari ya afku a Sabongari, Kano: kafa Jam’iyyar ’Yan Arewa Masu Aƙidar Cigaba (NEPU) Sawaba da wasu samari takwas masu kishin qasa suka yi. Ranar 8 ga Agusta 1950, Abba Mai Kwaru da Bello Ijumu da Baballiya Manaja da Musa Kaula da Abdulƙadir Ɗanjaji da Garba Bida da Mudi Sipikin da kuma Magaji Ɗambatta suka haɗu a gidan Bello Ijumu, mai lamba 9, a Titin Ibadan a Birnin Kano, don kafa jam’iyyar da za ta ƙalubalanci zaluncin mulkin haɗin guiwar masarautun gargajiya da ’yan mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya.
NEPU ba jam’iyyar siyasa ce ba kawai; wani gangamin ne na masu aƙidar burin ’yantar da Talakawa daga zaluncin da ake yi musu, bisa jajircewar gyara tsarin masarautun gargajiya a Arewacin Nijeriya da samar wa qasa ’yanci. Duk da NEPU jam’iyyar Lardin Arewa ce, waɗanda suka kafa ta sun kasance masu hangen nesa da kishin ƙasa.
- Akidar Siyasar Malam Aminu Kano Da Ta ‘Yan Siyasar Yanzu A Mizani –Farfesa Habu
- APC Da PDP, Duk Kanwar Ja Ce -Kwankwaso
Lokacin kafa ta da mahangar da take wakilta, sun wajabta a yi zurfin tunani game da yanayin da shugabancin siyasa ya tsinci kansa a Kano. Mafi cancantar mubaya’a ga cikar NEPU shekaru saba’in da biyar, ita ce a yi karatun ta-natsu game da rugujewar tsarin sahihin shugabanci, maimakon a vata lokaci ana ta biki cike da hargowa da hayaniya maras amfani.
Ta waɗanne hanyoyi mafi shaharar ƙungiyar siyasa a Kano, Kwankwasiyya, ta haɗu da, ko ta kauce wa aƙida da manufofin NEPU Sawaba waɗanda aka san Kano bisa turbarsu? Ta yaya aka maye gurbin dabarun gwagwarmayar tabbatar da adalci, tsarkake aqida da kawo daidaito a cikin al’umma da siyasar tumasanci, bautar ganin ido, da baje kolin kasuwancin siyasa?
Wannan sharhi ya yi bayanin harkokin siyasar da ake ciki da tsarin tafiyar da shugabancin da ya biyo bayan zamanin NEPU a Kano, musamman yadda siyasar aƙida ta zakuɗa wa kasuwancin siyasa wuri ya yi zauna dirshan a tsakanin al’umma.
Ta hanyar waiwaye da hararo tarihi, sharhin ya tattauna yadda aka gurɓatar da siyasar sadaukar da kai ta zama siyasar saye da sayarwa har aka samu bunƙasar Rabiu Musa Kwankwaso a fagen siyasar Kano. Bugu da ƙari, an bayyana illolin da suke tattare da irin wannan mummunan sauyi ta fuskokin siyasa da tattalin arziki da zamtakewa. Sharhin ya yi kira da babbar murya ga masu ruwa da tsaki a cikin al’umma don kowa ya kawo tasa gudummawar har a farfaɗo da kyakkyawar siyasar aqida irin wadda tarihin NEPU da PRP ya shimfiɗa a Kano.
NEPU: Mai Tarihin Ceton Al’umma
Manufofin NEPU da aka bayyana a Ƙudurin Sawaba na 1951 su ne tubalan da aka gini aƙidar ma’abota siyasar gwagwarmaya da kawo sauyi a Arewa. Manufofin sun ƙuduri niyyar:
Wargaza halascin mulkin gado kamar yadda tsarin Masarautun Gargajiya ya tanada; Fahimtar tare da bayyana rashin jituwar rundunar ƙawancen ’yan koren Turawa da talakawa a matsayin yaƙi tsakanin azzalumai da abin zalunta;
Dimokuraɗiyyantar da hukumomin mulki su kasance makaman ceto al’umma;
Ƙalubalanci zaluncin sarakuna ta hanyar wayar da kan al’umma su rungumi matakan juyin juya-hali; Shimfiɗa sabuwar aƙidar mulki wadda za ta tabbatar da adalci da ’yanci da kare mutuncin ɗan’adam.
Kwararar aƙidar NEPU da Jam’iyyar Ceton Al’umma (PRP), musamman a ƙarƙashin jagorancin ma’abocin ilimi da ɗa’a irin Malam Aminu Kano, ta dasa saiwoyin siyasar gwagwarmayar kawo gyara da sauyi don tabbatar da adalci. Ajiye aikin Aminu a Oktoban 1950, don ƙalubalantar cin hanci da rashawa da wariya, da ci da gumin wani, yadda tsarin Masarautun Gargajiya ke tafiya; ɗaura yaƙin murƙushe zaman ta-ci-barkatai da al’umma ke ciki ne. Tarihin siyasarsa cike yake da mutunci, mahawarar ilimi, da neman daidaiton al’umma; waɗannan abubuwan ne suka haifar da aƙidar siyasar da Kano ta taso a cikinsu shekaru aru-aru da suka wuce.
A Jumhuriya ta Biyu, PRP ta bunƙasa ayyukan NEPU har gaggan masu ilimi irin su Chinua Achebe da Wole Soyinka da Bala Usman suka rungume ta. PRP ta faɗaɗa harkokin tallafawa raunana, da yin tasiri ga dubban mutane har suka shiga siyasa, da tabbatar da Nijeriya a matsayin qasa mai cikakken ’yanci maimakon ’yar koren Turawan Yamma da Amerikawa. Kirayen PRP ga al’umma a fili yake: siyasa ba rumfar saye da sayarwa ba ce a kasuwa. Siyasa fagen dagar kare mutuncin ɗan’adam ce.
Ta’adin Sojoji ga Siyasar Aƙida
Farmaki ga siyasar aƙida ya faro ne a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida (1985–1993). Ta hanyar tursasa wa mutane shiga jam’iyyu biyun da soja ya kafa: Jam’iyyar Masu Sassaucin Ra’ayi (NRC) da Jam’iyyar ’Yan Gaba-daigaba-dai (SDP), Babangida ya tumɓuke jijiyoyin siyasa daga hurumin al’umma. Waɗannan jam’iyyun soja sun kasance masu ƙishin ruwan sahihiyar aƙida, kuma an samar da su don su haɗe kawunan masu ido da tozali wuri guda, maimakon bunƙasa harkokin dimokuraɗiyya.
Makircin sojoji na kwance auren da yake tsakanin siyasa da al’umma ya haifar da mummunan tsarin gina dillalan siyasa da biyayyar kuɗi hannu da bautar gumakan siyasa masu ɗauke da sunan shugabanni ba bisa cancanta ba. Zakuɗawar jama’a daga ɓangaren siyasar aqida zuwa dandalin kasuwancin siyasa ba bakatatan ya afku ba, tsararren lamari ne. Ɓangarori da jami’an tafiyar da harkokin jam’iyya suka kasance wulaƙantattu, gatanci da son kai suka maye guraben aƙida da cancanta. Don haka, kamfen a siyasa ya koma ciniki da kasuwanci a maimakon yunqurin kyautata rayuwar al’umma da gina ƙasa.
Kano, wurin da ya kasance cibiyar aƙida da yunƙurin tabbatar da adalci a tarihin siyasar Arewacin Nijeriya, ya rikiɗe zuwa dandalin baje kolin kasuwancin siyasa. Nan da nan sai wasu irin shugabannin siyasa, barbarar yanyawa suka ɓullo, ba ta hanyar jajircewa bisa aƙida da sadaukar da kai ba; sai ta hanyar tsananin son kai da haɗamar mulki, da damfarar siyasa. Sai ƙararrawar gwanjon muƙaman jam’iyya da na gwamnati, ga masu kuɗi hannu ta binne kirarin shelar yunƙurin ceton al’umma da jarumtaka. Nan da nan sai ya kasance mafiya muhimmanci da dacewa a harkokin siyasa ba su ne waɗanda suke da kyawawan halaye ba, su ne masu hannu da shuni ko ’yan lele.
Taka Rawar ’Yan Uku: Shekarau da Ganduje da Kwankwaso
A tafiyar da harkokin siyasa a Kano, bayan shuɗewar PRP, mutane ukun da suka fi sauran ’yan siyasa tasiri har tsawon shekaru ashirin da biyar su ne: Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje da kuma Rabiu Musa Kwankwaso. Kowannensu ya yi zango biyu (shekaru takwas) a karagar mulkin Jihar Kano. A wuyan gabaɗayansu alhakin gurvacewarsu siyasar Kano, daga gwagwarmayar tabbatar da aƙidar gyaran al’umma da gina ƙasa zuwa baje kolin kasuwancin siyasa, ya rataya.
A ’yan kwanakin nan, an samu tarayyar ra’ayin masu sharhi a kan harkokin siyasa, da al’amuran yau da kullum, ƙwararru da masana, kamar tsohon Mai Bayar da Shawara ta Musamman kan Harkokin Addini a zangon farko na mulkin Kwankwaso
(1999–2003), wanda ya sake riƙe muƙaman Kwamishina a Ma’aikatun Ilimi Mai Zurfi da Harkokin Addini a gwamnatin Ganduje (2019–2023), Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) da Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Malamai ta Jihar Kano, Ibrahim Khalil, cewa alhakin cigaban gurɓatar tarbiyyar matasa da rugujewar jam’iyyun siyasarmu, a matsayinmu na al’umma, kacokan ya rataya a wuyan waxannan hamshaƙan ’yan uku, saboda rawar da suka taka ko suke takawa har yanzu.
Tabbas, kowane ɗayansu yana da irin nasa gararin a matsayinsa na mutum, ko na ɗan siyasa. A daidai nan, zan bayyana yadda jama’a suke kallon alaqarsu da taɓarɓarewar harkokin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa a Jihar Kano. Zan kuma faɗi fahimtata da tasirin ayyuka da tsare-tsarensu na siyasa ga al’umma.
Don kore shakka, ba ni da matsala da kowane ɗayansu. A gaskiya, ina da kyakkyawar dangantaka da Ganduje. Ni da Shekarau muna matuƙar mutunta juna. Dabarun Kwankwaso na zaburar da mutane da cafke su gam-gam da riƙe akalar biyayyarsu, na ba ni sha’awa ƙwarai da gaske. Duk da haka, ƙaunar Kano da kasancewa xalibin tarihi sun rinjayi sauran al’amura masu kai-kawo a zuciyata.
Ibrahim Shekarau
Mutane na ɗaukar Shekarau mai ƙarancin laifi a kan sauran. Ba shi da ɗagawa. Bai yi girman kai ba ko lokacin da yake gwamna. Shigarsa ofis ba ta haukata shi da giyar mulki ba. Ba mai kallon sa a matsayin ɓarawo. Ba a zarge shi da sace kuxaxen Ƙananan Hukumomi kai-tsaye ko ta dabarun ƙirƙira asusun haɗin gwiwar boge don manyan ayyuka na musamman ba.
Duk da haka, kasancewarsa ɗa ko uban Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi (MSS) a lokaci mai tsawo; kuma wanda guguwar farfaɗo da Shari’a ta wurgo shi kan kujerar gwamna, saɓanin mutumin da ya gada mai yi wa harkar farfaɗo da Shari’ar Musulunci riƙon sakainar kashi, a zamaninsa an ga gaggawar ƙoƙarin ‘Musuluntar’ da tsarin tafiyar da gwamnati da hukumominta. Shekarau ya zurarar da lalitar jama’a wurin biyan buƙatun ƙungiyoyin addini da na mutane masu kai-kawo da siffar wakilcin addini. Ɗauraye ayyukan siyasar Shekarau da ruwan addini ya sa wasu zaton a fannin addini ya samu digirinsa maimakon lissafi.
Duk da tsantseninsa na riqe amanar dukiyar al’umma, ana zargin sa da rauni wurin kare martabar asusun gwamnati. Bai kasance mai sa cikakken ido da tsawatarwa ko hukunta mavarnata a cikin ma’aikatansa ba; duk da an zargi wasu da taɓargaza da ha’inci.
Haka kuma, ’yancin da ya ba ƙananan hukumomin, lokacin mulkinsa, ya tona asirin zurfin almubazzaranci da ƙwarewar cin rashawar jami’ansu.
A gaskiya Shekarau bai yi nasarar gabatar da muhimman ayyukan inganta rayuwar al’umma ba a lokacin mulkinsa; hankalinsa ya fi karkata wurin ƙoƙarin ‘gyaran zukatan mutane’ ko ‘a daidaita sahu.’ Ya ƙirƙiri hukumomi barkatai irin su Hukumar Shari’a da Hukumar Hisbah da sauransu a yunƙurinsa na neman cim ma wannan buri.
Duk da rauninsa a harkar shugabanci, Shekarau ya fahimci bambance-bambancen da ke cikin al’umma kuma ya yi ƙoƙari wurin kwatanta adalci da sasanci a tsakaninsu. An samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zamaninsa maimakon zaman ɗar-ɗar da ake danganta Kano da shi, a lokutan baya.
Bayan kyautata wa ƙungiyoyin addini, Shekarau ya ba da kulawa da tallafi mai gwaɓi, masu kama da almubazzaranci, ga masarautu da sarakuna. Wannan ne ya sa Sarkin Kano, Ado Bayero, ya naɗa shi Sardaunan Kano a matsayin godiya ko tukuici. Ƙawancensa da masarautun gargajiya ya saɓa wa manufofin NEPU da PRP, duk da cewa masarautun sun kasance ɓurɓushin al’ada da tarihi.
A matsayinsa na ɗan siyasa, Shekarau daidai yake da Kyanwar Lami: ba cizo ba yakushi; wato ba yabo ba fallasa. Ya yi cincirundon mabiya rantsattsu a baya, amma sannu a hankali ya watsa su saboda rashin ingantaccen tsarin shugabanci da yawan tsalle-tsalle tsakanin jam’iyyu a matsayinsa na jagora.
Ba a ɗauke shi mutum kaifi ɗaya ba. Kuma ana zargin sa da yin alƙawura masu harshen damo.
Tsirarun mabiyansa da suka rage, suna cewa babbar matsalarsa ita ce, sha’awar ya daɗaɗa wa kowa, wanda a mafiya yawan lokuta, sai ya munana wa kowa. Wataqila shi ya sa yake yin alƙawura waɗanda ba zai iya cika su a lokutan da suka kamata ba.
Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje, a ra’ayin jama’a, shi ya fi sauran wahalar kwatance. Misali, yana da faranfaran da mutunta kowa, tamkar dillalin alewa, sai dai walwalarsa ba ta nufin labarin zuciya a tambayi fuska. Don haka wasu suke yi masa kirarin “macijin ƙaiƙayi, sari ka noƙe.” Mutum ne mai matuƙar waskiya da zilliya da zamiya. Ana zargin ya ɗauki yaudara da riya a matsayin farillan hulɗarsa da dangantakarsa ta siyasa da jama’a. Yana da haƙuri, ga wayo kamar dila, gami da hangen nesa.
Akwai alamun bai amince da kowa ba sai kansa. A matsayinsa na jami’in gwamnati, an ɗauke shi tamkar wata maɓuɓɓugar cin hanci da rashawa. Kwaɗayinsa na handama da wawura da babakere, ya wuce maganar haɗama, ya zama tamkar wani gawurtaccen mikin mutu-ka-raba a cikin ƙoƙon zuciyarsa.
Akwai masu zargin duk wata kwangila da gwamnati ta yi a lokacinsa, daga ɗinka wa ’yan jam’iyya kayan ashobi zuwa ginin gada, shi ne ɗan kwangilar. Misali, hotunan bidiyon da aka nuna shi yana karvar cin hancin daloli wurin wani xan kwangila, duk da ya ci gaba da ƙaryata ingancin zargin, idan ya tabbata gaskiya ne, ba a tava samun gwamnan da ya wulaƙanta kansa haka ba.
Duk da zargin zarmewarsa a harkokin son zuciya, ayyukan gine-gine da gwamnatinsa ta yi ingantattu ne bisa shaidar ƙwararru. Wato sun sava da ayyuka awon igiya masu muguwar tsada waɗanda gwamnatin Kwankwaso ta yi.
Saboda tsananin son kansa, ya kasa riƙe nagartattun ’yan siyasa masu mutunci a tawagarsa. Don haka ya gaza samun tabbataccen zatin kansa na siyasa, kuma yake rakuɓe cikin inuwar Kwankwaso a tsawon shekaru takwas da ya mulki Jihar Kano.
Yawancin abokan burminsa a siyasance sun kasance ’yan jagaliyar siyasa da zauna gari banza. Mutanen da ba su iya amfanar kansu balle su amfanar da wani. Ma’aikata masu amana da ’yan siyasa masu mutunci ba su da wata ƙima a gaban Ganduje, balle su sami ƙwarin gwiwar tafiyar da ayyukansu a tsanake.
Misali a lokacin babban zaɓen 2023, yaronsa da ya naɗa Shugaban Jam’iyyar Gamayyar ’Yan Cigaba (APC) a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, a fili ya roƙi kar Allah ya kiyaye masifar da za ta tashi idan zaɓen gwamna ya zo. Take addu’arsa ta karɓu, zaven ya zo aka kayar da su qasa wanwar da halastacciyar ƙuri’a.
Abin mamaki, a matsayinsa na gwamnan da ya yi shekaru takwas bisa karagar mulki, kuma tsohon shugaban jam’iyyar da take mulkin ƙasa, Ganduje ba shi da wata tawaga muhimmiya ta ’yan siyasa a tare da shi a Kano. Wannan ba ya nufin babu kilakin siyasa da ’yan iska da ’yan ta’addar da zai iya ɗauka haya, domin su yi masa kwangilar rashin mutunci, ko assasa mummunan tashin hankali, idan akwai buƙatar hakan.
Akwai ma’aikata da ’yan boko jingim masu takaicin irin damarmakin da Ganduje ya samu na ya gyara muhimman al’amura a Jihar Kano, ya watsar da gangan.
A cikin su ukun, ya zarta sauran ilimi; ƙwarewa; wayewa; dukiya da shekaru a lokacin da ya zama gwamna. Jimillar ayyukansa ba ta nuna ya fi sauran tsumma ba, balle ya kaxa musu kwarkwata. Biyayya ta fi cancanta samun Kyakkyawan sakamako wajen tafiyar da ayyukan siyasa da na gwamnati, a wurin Ganduje.
Abin mamaki, duk da mutane na ganin Ganduje a matsayin matsolo, akwai wasu zaɓaɓɓun mutanensa da abokan hulɗa waxanda yake yi wa aiken kuɗi a wasu lokuta, musamman a bikin ƙaramar Salla da babba, na kowace shekara.
Bisa la’akari da tarihin siyasar aƙida da shugabancin NEPU ya dasa a Kano, mutane na cike da mamakin shin mene ne dalilin cigaban gurvacewar harkokin shugabancin siyasa a Jihar Kano?
Rabiu Musa Kwankwaso
Cikin mutane ukun da ake zargi da alhakin gurɓacewar tarbiyyar matasa da zagwanyewar mutuncin siyasar aƙida, Kwankwaso ne kaɗai dirarren ɗan siyasar da yake ta ɗimbin magoya bayan da suke da tasiri a wurin iya juya akalar ko gurvata tarbiyyar siyasa a Kano.
Don haka ya zama wajibi wannan sharhi ya tattara hankalinsa a kan Kwankwaso da burin a fahimci yanayin alaƙarsa da tushen masifar da Jihar Kano ta faɗa ciki tsundum.
Yayin tattauna me ya haifar da kasuwancin siyasa har gurɓatar abubuwa ta rinjayi siyasar aƙida a Kano, wajibi ne a yi nazarin tarihin shiga siyasar Kwankwaso, dabarunsa na samun mabiya da bunƙasarsa a fagen siyasar jihar.
Shin Kwankwaso sahihin ɗan siyasa ne me burin gina al’umma, ko ɗan damfara ne, mai amfani da kidahumancin mabiyansa don ya ci da guminsu?
Amsa wannan tambaya zai fi sauƙi idan aka hararo yadda siyasa ta sauya kamanninta a Kano; daga gwagwarmayar ceton al’umma a ƙarƙashin jagorancin Aminu Kano, zuwa kasancewa kamfanin saye da sayarwar Kwankwaso don ya yi safarar mabiyansa, ya more ribar cinikin shi kaɗai, a ɓagas.
Ɗimbin masoyan Kano suna takaicin yadda al’muran siyasa suka taɓarɓare a jihar har mai ra’ayin riƙau irin Kwankwaso ya samu damar kafa kamfanin siyasa mai ɗauke da sunansa (Kwankwasiyya); kuma yake baje kolinsa a ciki yadda ya ga dama. Ya kamata a fahimci qaurace wa siyasa da sahihan mutane masu mutunci da kyakkyawar aƙida suka yi, ta ba Kwankwaso damar kwakwashe matasa da hure musu kunnen su yi masa leburanci, shi kuma a matsayinsa na madugu ya dinga amshe ladan ƙwadagonsu. Kura da shan bugu gardi da karɓe kuɗi!
Sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga.
Shin mene ne tarihin siyasar Kwankwaso da dabarun yaƙinsa, domin a fahimci yadda bunƙasarsa ta juya akalar siyasar Jihar Kano maimakon kyautata aƙidar gwagwarmayar neman ceto al’ummar qasa zuwa fafutukar ƙoƙarin neman mulki da tara dukiya don biyan buƙatar kansa.
Tarihin siyasar Kwankwaso ya fara daga zuwansa Majalisar Wakilai ta Taryya daga Mazaɓar Kura-Madobi-Garun Malam, a ƙarƙashin tutar SDP, a cikin Yuli na 1992. Ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar a lokacin da kujerar ta faɗo Jihar Kano. A 1994 ya ci zaɓen kai da halinka, zuwa Taron Tattauna Tsarin Mulkin Ƙasa, daga Gundumar Kano Ta Tsakiya.
A 1999, ya tsaya takarar fitar da gwani a PDP don samun damar tsayawa zaɓen gwamnan jiha wanda ake shirin yi. A ƙuri’un da ‘deliget’ suka jefa, Ganduje ya yi wa Kwankwaso fintinkau.
Nan take wani abokinsa, Hakimin Gabasawa, Aminu Babba Ɗan Agundi, ya kawo wa Kwankwaso ɗaukin gaggawa da haramtattun ƙur’un da ya ƙirƙira na boge a Mazaɓar Gabasawa; don haka aka ce wai ya yi nasarar kifar da Ganduje.
Wannan cin amana da su Kwankwaso suka yi, ya kusa wargaza jam’iyyar PDP a Jihar Kano. Abin mamaki, sai Ganduje ya rungumi ‘ƙaddara’ domin jam’iyya ta zauna lafiya, kar a yi uwar-watsi. Halin dattakon da Ganduje ya nuna, ya janyo masa farin jini da tausayi da ƙauna a wurin shugabancin jam’iyyar.
Idan da gaske, yadda mutane ke zargi, Ganduje ya tafka maguɗin ɓarar da su Kwankwaso a zaɓen gwamna na 2019, sai a ce ƙwaryar da ta tafi ce ta dawo. Wato an yi ramuwar gayya, ko an yi wa wanzami jarfa.
Daraktan Shirye-Shirye na Yaƙin Neman Zaɓen Kwankwaso (1999–2003), wanda ya naɗa Kwamishinansa na Ma’aikatar Kuxi, Ibrahim Ɗan’Azumi Gwarzo, ya tabbatar da sahihancin labarin maguɗin zaɓen da Aminu Babba ya tafka don a rinjayi Ganduje.
A cewarsa, ya yi amfani da wayoyinsa masu lambobi: 064-670095 da 064-670096, daga Farfajiyar Ƙidayar Zaɓe ya tattauna kai-tsaye da Hakimin Gabasawa, domin ya sanar da shi adadin haramtattun ƙur’un da ya kamata su ƙirƙira don runtuma Ganduje da ƙasa.
Ana ba Kwankwaso takara, sai ya zama dodo. Ya yi watsi da maganar adalci da daidaito a wakilcin ɓangarori ukun da suka zama tubalan gina PDP a Jihar Kano; wato NPN (ƙarƙashin Aminu Wali); Santsi (ƙarƙashin Muhammadu Abubakar Rimi); Taɓo (ƙarƙashin jagorancin Dauda Ɗan Galan da Musa Gwadabe).
Wannan cin amana da wulaƙanci na Kwankwaso ya firgita dattijan PDP ainun, har wasu suka soma nadamar ‘nasararsa.’ Haka suka ci gaba da zaman doya da manja har lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Gwamnan.
Kwankwaso ya ƙalubalanci dattawan da suka zaɓi Ganduje ya zamar masa ɗan takarar mataimakin gwamna. Ya yi wurgi da shawarar wanda suka amince a naɗa Sakataren Gwamnatin Jiha. Ya ƙi yarda da mutumin da suka zaɓa ya zama sabon Shugaban Jam’iyya don maye gurbin Yusuf Baita wanda ya naxa Kwamishinan Ciniki da Masana’antu.
Mai shugabantar tawagar dattawan, kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdu Dawakin Tofa, ya sanar da ni yadda Kwankwaso ya so ya yaudare shi a lokacin; ta roƙon a bar shi ya zavi ƙanin Dawakin Tofan, Mahmud Baffa Yola, ya zamar masa ɗan takarar mataimakin gwamna.
Sai Dawakin Tofa ya sanar da shi bai iya abin kunya da cin amana da rashin mutunci ba. Ashe tuni Kwankwaso ya gama tsara idan har Tofa ya amince a jingine Ganduje, to wani mutum daban, Bello Hayatu Gwarzo, zai ɗauka su yi takara tare ba Mahmud ba.
Shin ta yaya Kwankwaso ya yi mugun ƙarfi, har ya zama alaƙaƙai a siyasar Jihar Kano?
A gaskiya, duk da siffofin gazawar da suke tattare da Kwankwaso, akwai wasu dalilai da dabarun da suke ba shi rinjaye a kan abokan hamayyarsa tun 1999.
Misali, yana da ximbin dukiyar da ya tattaro ta hanyar amfani da kujerun da ya riƙe na muƙaman Gwamna da Ministan Tsaro da Mamba a Kwamitin Gudanar da Hukumar Raya Yankin Niger Delta (NNDC) da kuma Jakada na Musamman a Darfur.
Ya ƙware a shirin zaune na ‘kan a farga,’ a duk ayyukansa. Yana da naci da juriya. Yana da baiwar laƙantar iya tafiyar da harkokin siyasar mutane na can ƙasa; saboda yau da gobe ba ta bar komai ba. Ya fahimci “durƙusa wa wada ba gajiyawa ba ne.” Yana durƙusawar yaudara cikin gaggawa tare da ladabin yahudanci don neman biyan buƙatarsa.
Dabarunsa na tuntuɓar neman mabiya da qulla alaƙar din-din-din da su, sun dace da yanayinsa na jemage a cikin tsuntsaye, ko baƙauye ɗan birni.
Gogewarsa ta karatun boko da abotarsa da alqarya, sun mayar da Kwankwaso xan birni. A duk lokacin da ya gwamutsa da mutanen karkara sai ya juye, kuma ya saje da su ta fuskokin zantukansa da halayyarsa, da al’adarsa. Idan ta yi ruwa rijiya!
Samun ɗan siyasa mai dangantaka ta ƙuƙut da mutanensa na can ƙasa, babban jari ne gami da baiwa ta musamman. Wurin da gizo yake saƙa shi ne, ta wace hanya yake amfani da irin wannan dangantakar? A nan ake gane ɗan siyasar kirki da na banza.
Yadda yake tafiyar da mabiyansa akwai mamaki. Yana gutsuttsura su ne domin ya samu damar fahimta da mallake su, shi kaɗai.
Misali, malaman jami’a, ma’aikata, ƙwararru, tsofaffin jami’an tsaro, ’yan kasuwa, da sauransu, waɗanda suka miƙa ragamar wuyansu a hannunsa, ya tokare su a iya ƙananan hukumominsu; wurin gudanar da ayyukan ƙungiyar Kwankwasiyya.
Don haka, shi ne kaɗai ya san haƙiƙar abin da yake afkuwa a cikin kowace ƙaramar hukuma da sauran sassan jiha bakiɗaya. Kwankwaso ba shi da muƙaddashi ko wani muhimmin kwamiti mai alhakin sa ido ga ’ya’yan ƙungiyar Kwankwasiyya, jumullarsu. Duk kwamitin da ya kafa don yin wani aiki kwatankwacin wannan sai ka tarar na jeka-na-yi-ka ne, da gangan.
Na fahimci waɗannan dokokin shiga Kwankwasiyya waɗanda a kundinsu babu rubutattun haruffa, sai ishara ko aiki da hikima, ta hanyar tattaunawar sirri da wasu abokaina da tsofaffin abokan tafiyar siyasa waɗanda a ƙaddararsu an rubuto su a Kwankwasawa. Na tabbatar da wannan ra’ayi ta nazarin salon siyasar Kwankwaso da abokan tafiyarsa.
Ba ya sakin jiki da masu ilimin da suka san ƙimar kansu da girmama ’yancinsu; ba ya karsashin hulɗa da su. Idan ƙaddara ta haɗa tafiyarsu, sai ya yi nesa da su; ko ya yi musu zagon ƙasa don kar su yi tasiri ko tsawon rai a ƙungiyar.
Ƙungiyar Kwankwasiyya
Babu abin da ya haɗa Ƙungiyar Kwankwasiyya da ra’ayin siyasar aƙidar neman sauyi don kyautata al’umma da gina ƙasa. Babu wasu rubutattun manufofi ko taƙaitattun bayanai masu fayyace takamamiyar aƙidar Madugu, balle a gwada ta da aƙidu da manufofin sauran fitattun ’yan siyasar Nijeriya, ko na Afrika, ko na duniya.
Kwankwasiyya taro ne na tarkacen mabiya masu dogon buri da zaton samun mafita ta hanyar tarayya da maigidansu wanda furucin gafalallun cikinsu ke allantawa.
Rashin tarbiyya da sigar isgilancin ’yan Kwankwasiyya a matsayin ƙungiya, ke jawo mata farin jini da karɓuwa ga matasa, kangararrun, tsageru, jariran ’yan siyasa, turaye, da masu neman su ci banza a cikin al’umma. Don haka shugabansu a kullum yake amfani da su a matsayin karnukan farautarsa na siyasa.
Kwankwaso yana amfani da al’adar siyasar Kanawa ta sojan-sa-kai don ya ci moriyar mabiyansa a matsayinsu na leburori ko karnukan farautarsa.
Tabbas a cikin ’yan Kwankwasiyya akwai mutane ƙalilan gogaggun ’yan siyasa; ko masu mutunci da hankali; ko ƙwararru waɗanda ba su damu da kare darajarsu ko ƙimar gudummawarsu ba. Akwai zargin tilas sai mutum ya ƙasƙantar da kansa, ko wofantar da ni’imomin da Allah ya yi masa, kafin Kwankwaso ya amince da biyayyarsa.
Furta kalmar “dimokuraɗiyya cikin gida” haramun ne a qungiyar. Babu tattaunawa game da adalci ko tabbatar da gaskiya a lokacin rabon muƙamai ko tsayawa takarar zaɓe. Yadda Madugu ya dama haka za a sha. Sai ɗan Musa!!!
A mafi yawan lokuta, bayar da irin waɗannan damarmaki sai wanda aka amince da makantar biyayyarsa. A wasu lokutan kuma suna zama hajar sayarwa kuxi hannu, musamman idan akwai baƙuwar fuskar da ta shigo ƙungiyar da ƙaruwar jakar tsaba a maqale a hammatarta. Zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri. Wannan ne ya sa babu mai iya cewa “uffan” ga kowane irin ɗanyen hukumcin da Madugu ya yanke.
Ƙungiyar Kwankwasiyya daidai take da rayuwar kurkuku a ƙarƙashin kulawar wani ƙasurgumin tantiri, wanda bai amince wa na tsare su sami sukunin tattaki ko tunani ba.
Dillancin Siyasa da Sayen Hannun Jari
Kwankwasiyya tana kama da matacciyar ƙungiyar nan ta A Cicciɓa Buhari (TBO); wadda muradinta na din-din-din shi ne neman hanyar da za a kai angonta ɗakin amaryarsa, ba tare da wani tanadi ko tunanin makomar miliyoyin mabiyansa ba.
A matsayinsa na dillalin siyasa, Kwankwaso na ɗauke da mabiyansa a cikin jakar hannu da niyyar sayarwa ga mai buƙata don ya azurta kansa.
A wasu lokutan yana iya bayar da Kwankwasawa haya ko jingina ga wata jam’iyya ko wani mutum a bisa alƙawarin za a tsayar da shi takarar shugaban ƙasa ko mataimaki, gwargwadon yadda kasuwar ta kaya masa.
A gaskiya, Kwankwaso ya jahilci me ake nufi da aƙidar siyasa balle ya zama sahihin jagora a siyasance. Ayyukansa na siyasa sun tabbatar da shi a matsayin dillali ko sojan haya.
Wannan ne ya sa duk tsalle-tsallen shigarsa da fitarsa cikin jam’iyun siyasa yana ɗauke da Kwankwasawa danqare a cikin kwantena, a matsayin hajarsa. Don ko sun yi rajista a jam’iyyar ko ba su yi ba, su ba ’yan jam’iyya ba ne.
Misali, shigarsa Jam’iyyar Jama’a ta Sabuwar Nijeriya (NNPP) da tatsuniyar tsayawarsa zaɓen shugabancin ƙasa a 2023, ya bar hajarsa tana maƙale da sunan shugabancin PDP na Jihar Kano. Wato kayan da aka yi gwanjon su Nyesom Wike ya biya Kwankwaso da dalar Amurka, amma ya bar su a shagon PDP kafin lokacin amfaninsu ya zo.
Da lokacin ya yi, sai Wike ya karɓe su a Abuja a matsayin ‘deliget’ na PDP daga Jihar Kano, ko kuma sojojin hayar da ya biya Kwankwaso don su taya shi yaƙar Atiku a zaɓen fitar da gwani na PDP. Waxannan marasa kunyar sai da suka gama qwadagon kwangilar da Wike ya ba Kwankwaso a PDP kana suka tarar da helimansu a NNPP.
Har ila yau, lokacin da babban zaɓen 2023 ya zo, jam’iyyar APC da ɗan takararta APC, Bola Tinubu, sun sake ɗaukar kwangilar Kwankwaso sojan haya, don ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a NNPP da burin mutanen Jihar Kano su jefa masa quri’a maimakon su zaɓi Atiku ya zama shugaban Nijeriya. Autan fikafiki lalata abokin tashi.
A matsayinsa na sojan haya, abubuwan da suke motsa gurɓatattun ayyukan Kwankwaso na siyasa sun haɗa da: ƙyashi da haɗama da ƙiyayya da kuma cin amana a kowane mataki ya samu kansa. A cikin waɗanda suka tsaya wa NNPP takarar gwamna a shiyyar Arewa maso Gabas, akwai wanda yake cike da labarin cin amana da ha’incin da yake zargin Kwankwaso ya yi masa a jharsu har gwamnan APC ya yi nasara a kansa.
Babban burinsa ya yi fancale ga duk ɗan Arewan da yake da haske ko alamun nasara a takarar kujerar shugaban qasa ko ta mataimaki; ta hanyar amfani da makafin mabiyansa don su tokare mutanen da suka fi shi kyakkyawan shiri ko cancanta ta kowace irin fuska. Abin takaicin, da sunan Kanawa ake tafka wannan rashin mutuncin.
A matsayinsa na haramtaccen Gwamnan Kano zango na uku, ta hanyar dabaibaye Abba Gida-gida, akwai zargin Kwankwaso ya mayar da baitul-malin Jihar Kano injinsa mai aman kuxi (ATM). Wannan ne babban dalilin ƙirƙirar Kwankwasiyya don ya samu makamin dasa sharri da yaudara da damfara da burga da kuma ƙulla dangantakar kasuwancin siyasa idan an samu masu sha’awar zuba jari.
Kwankwaso bai san yin biyayya ga wani ba sai kansa. Ba shi amfanar da kowa. Ƙwarewarsa a haɗamar siyasa da cin amana ta shahara. Duk wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takarar shugaban ƙasar da ya gayyaci Kwankwaso su yi tafiya tare, ya gama kashe kansa. Babu mai hankalin da zai amince masa.
A yanayin siyasar Arewacin Nijeriya, ƙungiyar Kwankwasiyya daidai take da ciwon daji (kansa). Ta hanyar rungumar ladubban siyasa da juriya da kyakkyawan tsari da sadaukarwa da ingantaccen quduri a tsakanin ’yan siyasa masu ruwa da tsaki, wato abokan hamayyar Kwankwaso a Kano, ta’annatin Kwankwasiyya ga sauran al’umma zai zama tarihi.
Tunanin Kwankwaso ya fi ƙarfin kaye a dandalin siyasar Kano tatsuniyar banza ce. Abubuwan da ake bukata domin a ci nasarar tumurmusa shi a qasa, sun haɗa da: ƙawancen gaskiya, shiri cikin hikima, sadaukarwar masu ruwa da tsaki a sabuwar tafiya, da burin ta yi nasara; kwalliya ta biya kuɗin sabulun kowa baki ɗaya.
A matsayinsa na gogaggen ɗan fancale, ko mai taka bakin faranti ga duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa ko mataimaki daga Arewa, a shirye Kwankwaso yake a ɗauke shi sojan haya don rashin sanin mutuncin kansa.
A halin yanzu, watakila ya ƙura idanunsa a kan wasu taurarin siyasar Arewa waɗanda ake hasashen suna sha’awar tsayawa takarar shugabancin ƙasa ko mataimaki, irin su Atiku Abubakar da David Mark da Aminu Waziri Tambuwal da Nasir El-Rufai da kuma Kashim Shettima. Zai iya kai wa kowannensu duka, ko ya soke shi da wuqar siyasa ta baya, idan cinikinsa da Bola Tinubu, ko da wani ɗan takarar shugabancin qasa daga Kudu ya faɗa. Mu bi shi a hankali don mu fahimci wace alƙiblar zai fuskanta a 2027.
’Yan siyasar Arewa da dama suna zargin babu dogaro da Allah a tsarin Kwankwaso na haɗamar neman abin duniya. Don haka, duk wani matsayi a ƙarƙashin ikonsa, na masarautun gargajiya ko na zamani, na sayarwa ne ga wanda tayinsa ya fi tsoka. Masu wannan zargi na kafa hujja da tataɓurzar da ake ciki a Masarautar Kano, wadda ta jima da sarakuna biyu, ’yan’uwan juna. Akwai alamun ginshiƙin siyasar Kwankwaso ya yi daidai da karin maganar “kare da kuɗinsa.”
Ko kaɗan bai dace a xauki Kwankwaso a matsayin sahihin shugaban siyasa ba, wato Jagora. Halayensa na mai kula da ayarin fatake ne, wato Madugu, kamar yadda kayayyakin da yake sayarwa a kamfaninsa na kasuwancin siyasa suke kiran sa.
Kamfanin Kwankwasiyya da dillalinsa sun jahilci me ake nufi da aƙidar siyasar gyaran ƙasa da gina al’umma. Kwankwaso bai fahimci sahihan hanyoyin da ake bi don shimfixa adalci da yi wa siyasa garambawul ba; balle kuma dilolin da yake sayarwa waɗanda a kullum suna cikin sito a kulle kafin zuwan ’yan sari.
Lokacin da na yi tunanin rubuta wannan sharhi don murnar cikar NEPU shekaru saba’in da biyar da kafawa, sai na tambayi wani dattijo ɗan Kwankwasiyya mene ne alaƙar ƙungiyarsu da NEPU ko PRP, wurin ba ni amsa sai ya ce:
“Alaƙar Kwankwasiyya da NEPU ko PRP ita ce kwaikwayon sanya jar hula, kawai.”
Bunƙasar masifun da matasa ke fuskanta, na rashin alƙibla ko mafita da shaye-shaye; ya sa biranen Arewacin Nijeriya ciki har da Kano, sun zama maƙyanƙyasar ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ’yan iskan gari. Ashe mutane irin su Kwankwaso, masu sha’awar makauniyar biyayya mai rahusa, ba za su rasa samun mabiyan da za su mallake da sunan siyasa ba. Don haka, ya wajaba mutane masu adawa da irin tsarin Madugun Kwankwasiyya su dunƙule wuri guda tare da ƙirƙiro wata sahihiyar hanya wadda za su bi don su magance matsalolin da suka yi wa al’ummar Kano da siyasarta tarnaqi, har da taimakon Allah a ci nasara.
Tabbas, Kwankwaso xan kwangilar siyasar saye da sayarwa bai cancanci a siffanta shi da magajin Malam Aminu Kano a tarihin siyasar Arewacin Nijeriya ba. Bugu da qari, Kwankwasiyya a matsayinta na qungiyar mutane masu alfaharin yi wa kawunansu kirarin su ne “makafin ɗan Musa,” ba ta da wata alaqa ko kaxan da kyakkyawar aƙidar siyasar sadaukar da kai da gwagwarmayar neman tabbatar da adalci wanda jam’iyyun NEPU da PRP suka haifar a tarihin siyasar Kano tun 1950.
Cin nasarar Kwankwaso na baje kolin kasuwancin siyasa, ba ya samuwa sai a gurɓatacciyar ƙasa, wulaƙantacciya, maciya amanar raunanan mutanenta, irin Nijeriya.
Mafiya yawan nasarorin Kwankwaso a matsayinsa na gwamna sun faru ne a zangonsa na farko (1999–2003), wato lokacin da ya yi aiki da mutane ƙwararru, masu mutunci da kishi da cancanta da sadaukar da kai a cikin majalisarsa ta zartaswa. Lokacin kan mage bai waye ba.
Zangonsa na biyu da wanda yake kai yanzu na uku da sunan Abba Kabir Yusuf; ana kwatancensu da ƙwarewa a cikin ayyukan yaudara da damfara da cin amana da yashe asusun jama’a ta hanyar ƙirƙiro wani haramtaccen tsarin samartakar vera mai suna: Asusun Haɗin Gwiwar Gwamnatin Jiha da na Ƙananan Hukumomi. Mafiya rinjayen ayyukan da ake gudanarwa ta wannan asusu babu su a ƙasa. Don suna da layar zana. Babu wanda yake iya ganin su sai mai wankin ido, kamar Madugu da lamuntattunsa.
Cikin irin ayyukan da yake alfahari da su, wasu tun a zangonsa na farko, kamar: tituna kilo mita biyar-biyar a qananan hukumomi; sikolashif don karatu a ƙasashen waje; almarar tsayawa takarar shugabancin ƙasa; asusun haɗin gwiwa don wadata asibitoci da magunguna; katafarun gadoji a cikin birnin Kano; da kafa wasu cibiyoyin ilimi na boge; misali, Cibiyar Wasanni a Kura, dukkaninsu hanyoyin sace kuɗaɗen al’umma ne kai-tsaye da rana tsaka.
Misali, kwanakin baya, tsohon Sakataren Gwamnatin NNPP a Jihar Kano, Baffa Abdullahi Bichi, ya furta cewa idan ya buɗe bakinsa game da sace-sacen da ake yi a wannan gwamnatin ta Kwankwasiyya sai mutanen Kano sun kori Kwankwasawa da ruwan duwatsu. Ya yi alqawarin amayar da duk abin da ya sani bisa dogaro da rubutattun bayanai idan lokacin yin hakan ya zo. Muna ji, muna gani, muna kuma saurare.
A zaton Kwankwaso yana da wayon da zai wofantar da hankali da tunanin kowa a kullum. Farfagandarsa ba ta hana mutane fassarar gwamnatinsa ta NNPP da sunan daular gafiyoyi ko dandalin samartakar ɓeraye ba.
A kidahumancinsa, watakila har da jahilci, bai san kifi na ganin sa mai jar koma ba. Lallai gobe za a sha kallo, idan tarko ya kama burgu, asiri zai tonu.
Mutane da yawa sun ɗau Kwankwaso mai girman kai saboda zaton ya fi kowa. A gaskiya ban amince da wannan ra’ayin nasu ba.
Kwankwaso na fama da ƙalubalen tunanin gazajjen mutum saboda rashin cancantarsa a fuskokin shugabanci masu yawa da kuma daƙiƙanci. Wannan dalilin ne ya sa shi ƙaryar yana da digirin digirgir, lokacin da ya zama gwamna a 1999. Mutumin da Allah ya girmama da zama Gwamnan Kano, kuma mai cikakken hankali, ba zai shara irin wannan ƙaryar ba don babu.
Gazawarsa, watakila da rashin samun cikakkiyar tarbiyya a ƙuruciyarsa, sun sa shi nishaɗin wulakanta muhimman mutane masu mutunci waɗanda kowa ke girmamawa bisa cancanta a cikin al’umma. Misali, ya ci mutuncin Sarkin Kano, Ado Bayero; ya yi wa Aminu Ɗantata rashin kunya; ya wulakanta Abubakar Rimi; ya muzanta ubansa na rana wanda ya tsamo shi yana gantali a karkara ya koya masa siyasa, Hamisu Musa; ya yi wa malaman addini ashariya waxanda suka yi tir da halayyarsa.
Ayyukan Kwankwaso na taɓargaza sun zarce girman kai. Ya kamata iyalai da masoyansa su fara tunanin hanyoyin da za su bi don shawo kan al’amarin. Allah ya sa a dace. Amin.
Kwankwaso ne, shi kaxai jal, yake da kaso mafi yawa cikin gurɓacewar tarbiyyar siyasa a Jihar Kano; da raunana jam’iyyunta; da yaudarar matasanta; wanda a dalilin haka harkokin siyasa suka zama baje kolin saye da sayarwa a kamfanin Kwankwasiyya.
Idan mutane masu mutunci da amana da tunani suka kawo sabon tsari ta fuskar tsarkake harkokin siyasa da tarbiyantar da matasa sanin muhimmancin siyasar aƙida da sadaukarwa, share Kwankwaso da kasuwancin siyasar kamfanin Kwankwasiyya, a dandalin siyasar Kano, da yardar Allah kamar yanzu ne.
Ya kamata duk sahihan ƙungiyoyin matasa da jam’iyyun siyasa da ɗaiɗaikun mutane masu aƙidar gyara ƙasa da gina al’umma su fahimci Kamfanin Kasuwancin Siyasa na Kwankwasiyya mallakar Kwankwaso wata guba ce da guguwar gurɓatacciyar dimokuraɗiyya ta yaryaɗa ta a Jihar Kano, kuma kowa ya guje ta.
Idan wannan sharhi ya sa wasu masu karatu tunani a kan zurfin gurɓacewar harkokin siyasar Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Kano, kuma suka amince da muhimmancin a jaddada manufofin jam’iyyun NEPU da PRP, sai in yi guɗar na cika burina.
NEPU! Sawaba!!; PRP! Nasara!!; Kwankwasiyya! Asara!!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp