Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Daga Shigar Marwa Ofis An Kama Hodar Iblis Da Ba A Taba Kamawa Ba

by Muhammad
January 21, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Marwa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta yi wani babban kamu. Jami’an NDLEA sun tare wani kilo 21.9 na hodar Iblis da aka yi yunkurin shigo da shi ta jirgi. Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata cewa jami’an Hukumar mai yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, sun yi kamun da ba su taba yin irinsa a lokaci guda ba.

Rahoton ya ce NDLEA ta yi nasarar dakile wannan muguwar kwaya ne a babban filin tashi da saukar jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke birnin tarayya Abuja. A ranar 18 ga Junairu, 2021, Mai magana da yawun hukumar, Jonah Achema, ya bayyana cewa sun cafke wasu akwatuna biyu masu dauke da hodar Iblis. Mista Jonah Achema ya ce hukumar ba ta taba tare kaya masu irin wannan yawa a lokaci guda ba.

A cewar jami’in, da yake bayani ranar Laraba, an gano wannan kaya ne a cikin wasu akwatuna da aka bari a jirgin Ethiopian Airline, ET 910, wanda ya taho daga Addis Ababa, kasar Habasha. “Da ake binciken jirgin, jami’an da ke lura sun zargi cewa akwai barnar da ake shirin yi bayan sun hangi akwatuna a ajiye ba tare da wani ya na ikirarin na sa bane.”

Jonah Achema ya cigaba da cewa: “Shugaban NDLEA ya sanar da ma’aikata su sa ido a kan kayan, kuma aka sanar da jirgin cewa hukuma ta na lura da akwatunan.” “Bayan an yi kwanaki babu wanda ya fito ya ce shi ya mallaki kayan, shugaban NDLEA ya tuntubi ma’aikatan jirgin, ya ba da umarni ka da a ba da kayan sai a gabansu.”

A karshe dole aka bude wadannan akwati domin a tabbatar da abin da yake ciki, sai ga hodar iblis (mai nauyin kilogiram 21.9), wasu boye a wata leda da aka kudundune a bargo.

An yi wa kayan tas ne a gaban jami’an NCS masu yaki da fasa-kwauri da DSS masu fararen kaya, da ma’aikatan harkokin jirgin sama, yanzu ana binciken mai wannan kaya. Kwanan nan aka ji shugaba Muhammadu Buhari ya nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA. Tsohon gwamna kuma sojan kasa, Mohammed Buba Marwa mai shekaru 67 ya zama sabon Darakta-Janar na hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi na kasa. Kafin yanzu, Marwa ya kasance shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da miyagun kwayoyi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Muna Godiya Da Addu’o’i Kan Garkuwa Da ’Yan Kasuwar Kwari – Dandago

Next Post

Jagoran Bunkure Da Mataimakansa Sun Yaba Wa Gwamna Ganduje Kan Cigaban Kano

RelatedPosts

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja Ranar Lahadi da ta gabata...

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri Biyo bayan harin da mayakan Boko...

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga Musa Muhammad, Abuja An kammala dukkan shirye-shirye don fara...

Next Post
Kadarorin

Jagoran Bunkure Da Mataimakansa Sun Yaba Wa Gwamna Ganduje Kan Cigaban Kano

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version