Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai koya muku yadda ake dahuwar Kifi na zamani:
- Dalilin Rahoton Farfesa Jega Na Bukatar Taimaka Wa Masu Kiwon Kajin Gidan Gona
- Ministoci Za Su Fara Gabatar Da Rahoton Ayyuka A Taron Manema Labarai Â
Abubuwan da za ku tanada:
Kifi karfasa, albasa, koren tattasai guda biyu, tattasai, taruhu, tumatur daya, tafarnuwa, jinja danyar citta kenan, magi, gishiri, kori, kayan kamshi, na’a na’a kadan, albasa mai lawashi, koriyanda kadan, black pepper, mai domin soya kifi.
Yadda za ki hada :
Da farko za ki wanke kifin sosai sannan ki barshi ya dan sha iska ruwan jikinsa ya tsane, sai ki zuba masa kayan dandano wato magi, gishiri, kori kayan yaji da duk wani abu da kike da shi na dandano ko kanshi ki cakuda shi kayan duk ya shiga jikinsa ki barshi ya yi kamar minti 10 saboda ya shiga jikinsa sosai.
Daga nan sai ki dora mai a wuta ya yi zafi ki dan sa albasa saboda ya yi kamshi, sai ki zuba kifin ki soya, bayan ya soyu sai ki kwashe.
Daga nan sai ki dakko tukunya ki dora a wuta ki zuba mai kamar ludayi daya idan ya yi zafi sai ki zuba tafarnuwa wanda dama kin bare ta kuma kin daka ta tare da jinja da kanunfari kidan soya su sama-sama, sai ki kawo tattasai da tumatur din wanda dama kin jajjaga su ki zuba, amma ba duka ba sai ki yi ta juyawa har sai ya soyu sai ki zuba magi, gishiri, kori kiji kome yaji. Sai ki kawo kifin nan da kika soya ki zuba a ciki ki dan juya su ki zuzzuba miyar akan kifin saboda ya shiga cikin kifin sai ki zuba koriyanda da dan kayan kamshi ki rage wuta ki barshi yadan yi kamar minti uku zuwa biyar haka, sannan kifin ya yi sai ki kawo albasa mai lawashi ki zuba ki rufe ki bashi kamar minti daya ya yi sai ki sauke shi ya yi.
Za ki ga dahuwar kifin ta yi kyau sosai ta ba da kalaga dadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp