Dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA, shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoninta a kewayen tsibirin Taiwan.
A cewar kakakin rundunar babban kanar Shi Yi, an tsara atisayen ne mai kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da masu sarrafa roka, ta yadda za su yiwa tsibirin Taiwan kawanya ta sassa daban daban.
- Kasar Sin Ta Nanata Adawa Da Matakan Tilastawa Da Nuna Babakeren Tattalin Arziki
- Tawagar Aikin Ceto Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin Ta Isa Myanmar
Shi Yi ya kara da cewa, makasudin aikin shi ne gudanar da sintiri na tabbatar da shirin ko-ta-kwana ta ruwa zuwa sama, da wanzar da karfin tunkarar dauki ba dadi, da kaddamar da hare-hare a kan teku da yankunan dake doron kasa, da iya kange muhimman wurare da hanyoyin teku, a matsayin gwajin kwarewar aiki ta dakarun sojin.
Kazalika, a cewar jami’in atisayen zai kasance wani salo na jan kunne mai karfi ga sassan dake rajin neman “’Yancin kan Taiwan”, kuma mataki ne halastacce da ya wajaba na kare ikon mulkin kai da dinke sassan kasar Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp