Connect with us

LABARAI

Dakatar Da Sanata Bulkachuwa: Shugaban APC Ya Yi Amai Ya Lashe

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC a Gudunmar Kafin Kuka/Tsakuwa/Kofar Gabas da ke karamar hukumar Katagum, Alhaji Sa’adu Muhammad ya yi amai ya lashe kan batun korar Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa daga jam’iyyar, yana mai shaida cewar gaban kansa yayi wanda hakan ya saba wa dokokin jam’iyyar don haka ya janye furucinsa na fari.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da shugaban Sa’adu da sakataren jam’iyyar a wannan Gudunmar Ibrahim Kubale suka fitar da safiyar yau, sun shaida cewar shugaban ya yi abin da bai dace ba domin bai tuntubi sauran shugabannin jam’iyyar APC wajen yanke wannan hukuncin nasa ba.

Don haka suna janye furucin dakatar da Sanata Bulkachuwa tare da bayyana cewar har zuwa yanzu shi cikakken mambar jam’iyyar na APC ne.

Idan za ku iya tunawa dai a ranar 9 ga watan Yuni ne shugaban ya kira wani taron manema labaru inda ya sanar da korar Sanata Bulkachuwa daga jam’iyyar da zarginsa da rashin tabuka abin a zo a gani.

Wakilinmu ya nakalto cewa, shi dai Sanata Bulkachuwa shine Sanatan da ke wakiltar mazabar Zaki, Gamawa, Itas-Gadau, Katagum, Jama’are da kuma Giade a majalisar Dattawan Nijeriya.

Sanarwar tana cewa; “Ni Sa’adu Muhammad (Shugaban jam’iyyar) APC a Gundumar Kafin Kuka/Tsakuwa/Kofar Gabas abin da muka yi a jiya (Ranar 9 ga watan Yunin 2020) a wajen taron da muka kira. Shugabannina na jam’iyyar sun kirani sun ce abun da na yi ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC. Ni kadai ba zan yanke hukunci ba.

“A saboda haka abun da na yi kuskure ne don haka yanzu na dawo da Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa cikin jam’iyyarmu ta APC. Da fatan jam’iyyar da wadanda abin ya shafa za su gafarceni,” A cewar takardar da shugaban ya fitar.

Baya ga hakan, a cikin zama da suka yi na gaggawa dukkanin shugabanin jam’iyyar a matakin Gundumar, sun nuna abin da shugabansu yayi a matsayin babban kuskure, inda suka shaida cewar komai da ke tafiya a jam’iyyance akwai shi a kundin tsari da dokokin tafiyar da jam’iyyar, don haka suka barranta da batun korar Sanata Bulkachuwa hadi da tabbatar da shi a cikin jam’iyyar ta APC.

Bayan ganawar sun kuma rattaba hannu kan takardar barranta da batun tsige Bulkachuwa suna masu shaida cewar shi din cikakken mambansu ne. shugabanin masu rike da kujeru daban-daban da yawansu ya kai mutum 20 sune suka sanya hannu a takardar barranta da batun na shugabansu tun da farko.

Ciki kuwa har da shi kanshi shugaban da yayi batun tun da fari suna masu nanata cewar Sanata Adamu Bulkachuwa har yanzu cikakken dan jam’iyyar ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: