Iyalai da dama na ci gaba da kai mari su kai gwauro, wajen kokarin samun damar yadda za su ciyar da iyalansu sau biyu ko sau uku a rana, wanda hakan ya zo daidai da gazawar gwamnatin kasar na cika alkawarorin da ta yi a 2024, na bayar da damar shigo da kayan abinci kasar.
“Na yi tsammanin tun a 2024, za a fara shigo da kayan abinci cikin kasar nan, amma hakan bai yiwu ba; yanzu haka ina batar da kashi 65 cikin 100 na abin da nake samu, wajen saya wa iyalina abinci; inda sauran kudin kuma ke tafiya a harkokin sufuri da sayen sauran kayan bukatun yau da kullum”, in ji wani magidanci mazaunin Jihar Legas, Ibrahim Wahab.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
- Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates
“Babu wani sauran kudi da ke raguwa a hannuna da za su ishe ni na zuba hannun jari”, a cewar Wahab.
Umarnin gwamnatin tarayya na bari a shigo da kayan abinci daga ketare, na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Yulin 2024, wanda ma’ikatar kudi ta fitar.
Ma’ikatar kudin, ta yi bayani kan dakatar da shirin bayar da damar shigo da kayan abinci cikin kasar da suka hada da; Shinkafa, Alkama, Masara da kuma wasu sauran kayan abincin.
Har ila yau, gwamnatin ta yi yunkurin bayar da damar shigo da kayan abincin ne, domin saukaka tsadar kayan abincin a Nijeriya.
Kudin fiton kayan abincin da suka hada da Shinkafa, Dawa da kuma Wake, ya kai daga kashi 5 zuwa kashi 30.
An Dora Alhakin Rashin Bayar Da Damar Shigo Da Kayan Abincin Kan Ma’aikatar Kudi:
Mai magana da yawun Hukumar Hana Fasakwuri ta Kasa, Abdullahi Maiwada; a makon da ya gabata, ya dora alhakin rashin bayar da damar shigo da kayan abincin a kan ma’aikatar kudi.
Maiwada, a hirarsa da jaridar BusinessDay a watan Satumbar 2024, ya dora laifin a kan ma’aikatar kudin; kan jinkirin wanzar da damar barin shigo da kayan abincin cikin kasar.
A cewarsa, ma’aikatar ta gaza mika jerin sunayen masu shigo da kayan da kuma sauran kamfanonin da suka cika sharuddan shigo da kayan abincin kamar yadda aka tsara.
“Kamar yadda Hukumar Kwastan ta Kasa, ta isar da tsare-tsaren shigo da kayan abincin; da ma’aikatar kudin ta amincewa tar da bayar da dama, da tuni an fara wanzar da shirin bayar da umarnin shigo da kayan”, in ji Maiwada.
Ya ci gaba da cewa, “Amma tun bayan da tsarin barin shigo da kayan ya fito daga ma’aikatar kudin, ya kamata a ce ta bayar da jerin sunayen wadanda suka cancanta su shigo da kayan”.
Wani bincike da jaridar ta BusinessDay ta gudanar ya nuna cewa, har zuwa watan Disambar 2024, ma’aikatar kudin ba ta tura wa Hukumar Kwastan jerin sunayen masu shigo da kayan ba; sannan kuma ba ta yi wani gamsasshen bayani ba.
Ci Gaba Da Fuskantar Barazanar Yunwa A Kasar:
Fiye da mutum 67 ne, ciki har da kanannan yara suka rasa rayukansu a turmutsutsun rabon kayan abinci a Nijeriya, daidai lokacin shagulgulan bikin karshen shekarar 2024; a wasu sassan kasar.
Wasu masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa, lamarin ya nuna a zahiri irin matsananciyar yunwar da talakawan kasar ke ci gaba da fuskanta.
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) a farkon shekarar 2024 ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya miliyan 33 ne za su fuskanci yunwa a 2025, ban da kuma wasu daga cikin ‘yan kasar kimanin miliyan 25 da suka fuskanci yunwar a 2024.
Mai magana da yawun shirin na WFP, Chi Lael; ya sheda wa manema labarai a taron Geneba na 2024 cewa, ‘yan Nijeriya da dama; abincin da za su ci ya gagare su.
Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, ta kirkiro da tsauraran matakai na bunkasa tattalin arzikin kasar, ciki har da cire tallafin mai da sauran makamantansu cikin daukacin fadin kasar.
A watan Nuwambar da ya gabata, an samu hauhawar farashin kayayyaki da kashi 34.6, da ya haura wanda aka taba samu cikin shekaru 28 a kasar, inda farashin kayan abinci ya karu da kashi 39.9 a shekarar 2024.
Wani rahoton girke-girke da aka fitar ya nuna cewa, a watan Satumbar 2024, magidanci mai ‘ya’ya biyar, na kashe akalla 21,300 cikin wata hudu idan zai dafa hadaddiyar Shinkafa, inda hakan ya karu da kashi 5.1 cikin 100.
A yanzu haka, ana sayar da buhun Shinkafa mai nauyin kilo 50; wacce ake shigo da ita daga waje da kuma wadda ake nomawa a kasar, kan Naira 100,000, inda farashinsu ya dara sabon mafi karancin albashin ma’aikata na Naira 70,000.
Bugu da kari, farashin kayan abinci da suka hada da Wake, Rogo, Dankali da sauransu, sun yi tashin gwauron zabi da kashi 100 cikin shekara daya tare kuma da kalubalen rashin tsaro da ya kara haddasa hakan.
Wani mai suna Daniel Brown, a fannin shigo da kaya cikin kasar ya bayyana cewa, “Tsadar kayan abinci ta karu a kasar, sakamakon rashin aiwatar da tsarin da gwamnatin ta gaza yi a watan Julin 2024”.
“Sai dai, rashin wanzar da wannan tsari; ya nuna a zahiri gazawar hukumomin gwamnatin taraya, wanda hakan ya kara jefa rayuwar talakawan kasar cikin wata matsalar daban”, in ji Brown.