Ko kun san waye Dakta Wandali Wanda Akafi Sani da Mr. Nigeria.
Dakta Dibal Arhyel Wandali kwararre ne a dakin gwaje-gwajen likitanci tare da gogewa wajen tsarawa, aiwatarwa, da lura da shirye-shiryen dakin gwaje-gwaje, kuma yana aiki a babban asibitin Biu, jihar Borno.
Yana aiki a matsayin masanin kimiyyar dakin gwaje-gwajen likitanci tun 1987, kuma yana farin ciki da alfahari da kasancewarsa dan Nijeriya.
Duk wadanda suka san shi sun tabbatar da haka. Yawanci yakan sanya kaya launin kore da fari, kuma duk ranar ‘yan cin kai, yakan tara ‘yan uwa da abokan Arziki ya yi musu liyafar murnar ranar Kasa, bugu da kari, daga bisani kuma sai ya rabawa makwabtansa da yara kyaututtuka.
Duk motocinsa an zana su da Launin kore da fara (alamar tutar Nijeriya).
#InsideNigeria.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp