Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya karbi daliban makarantar Kuriga da aka kubutar 137 a gidan gwamnatin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewar dalibai 137 da malami daya ‘yan bindigar suka sace kuma gaba daya an kubutar da su.
- Gwamnatin Kaduna Ta Karɓi ‘Yansanda Masu Horo Na Musamman 200 Da Motocin Yaƙi 2
- Fasahar Intanet 10 Da Mutum Zai Iya Koya Ya Ci Gajiyarsu Cikin Kwana 90
Tun a daren Lahadi dai aka kawo daliban Kaduna sai dai sun kwana ne a hannun sojoji, inda aka duba lafiyar su a asibitin sojoji kafin mika su hannun gwamnan jihar, a humkumance a ranar Litinin.
Babban kwamandan runduna ta daya da ke Kaduna, Manjo Janar, Mayirenso Saraso, shi ne ya damka daliban ga gwamnan jihar, kuma ya yi bayanin yadda aka kubutar da su.
Ya ce aikin hadin gwiwa ta hanyar hada karfin soji da kuma sasanci aka yi amfani da su wajen kubutar da daliban wadanda suka shafe kwanaki 16 a hannun ‘yan bindiga.
A yayin jawabinsa, gwamna Uba Sanin, ya ce asalin adadin daliban da aka sace da ma 137 ne ba 287 ba.