Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta bayyana cewa kawo yanzu kimanin daliabi 947,000 ne za su zana jarabawar cikin kwanaki biyu masu zuwa.
Dokta Fabian Benjamin, Shugaban Hulda da Jama’a na Hukumar, ne ya bayyana hakan bayan sanya ido kan yadda ake gudanar da jarabawar UTME tare da magatakardar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, da sauran su, a ranar Alhamis a Abuja.
- Mutum 6 Sun Mutu Yayin Da Tankar Mai Ta Yi Bindiga A Filato
- Zaben Adamawa: A Hukunta Kwamishinan Zaben Adamawa -Fintiri
Fabian, wanda ya ba da tabbacin cewa duk wanda ya yi rajistar jarabawar za a ba shi damar shiga wajen zana jarabawar, inda ya ce hukumar ta warware matsalolin fasaha da aka fuskanta a ranar farko a wasu cibiyoyi a fadin kasar nan.
“Wannan ita ce jarabawar da ta fi dacewa da muka dauki tsawon lokaci, amma na san da yawa za su so sanin abin da ya faru a ranar Talata, amma na san idan kuna cikin tsarin kuma kuna bin jarabawarmu, za ku san cewa rana ta farko ta kasance cikin tashin hankali, amma komai zai daidaita.
“Kuma wani tabbacin da muke son bai wa daliban Nijeriya shi ne cewa duk dan wanda ya yi rajistar wannan jarabawa, to tabbas za a ba shi damar yin jarabawar.
“A ranar farko an samu dalibai da suka kasa zana jarabawar saboda wasu lamura da suka shafi fasaha kuma mun sake sanya sunayen wadanda za su yi jarabawar, wasu kuma kamar yadda muke magana za su yi tasu jarabawar gobe.”
Ya kuma ce hukumar za ta sanar da sakamakon nan ba da jimawa ba.